Yau Daren Isra'i Da Mi'iraji 27 Ga Watan Rajab |
Yau Daren Isra'i Da Mi'iraji 27 Ga Watan Rajab
Isra'i da Mi'raj (Da Larabci : الإسراء والمعراج , al-'Isrā' wal-Mi'rāj ) su ne sassa biyu na Tafiyar Dare da Annabinmu Muhammadu (SAWW) Yayi a cikin dare guda a wajen shekara ta 621 Miladiyya wanda yayi daidai da shekara 27 Ga Watan Rajab a shekara 1 kafin Hijira. A Musulunci yawancin malamai sun yarda cewa tafiya ta jiki ce da ruhi.
Game da Isra'i da Miraj, an ambace shi a cikin surar Isra'i. A Isra'i, farkon dare, Jibrilu da ya zo wurin Annabi Muhammad (SAW) sannan ya hau Buraq, wanda ta fi jaki girma. A kan Buraq ya yi tattaki daga Makkah (Masjid al-Haram) zuwa Masallacin Al-Aqsa cikin dakika daya kacal, domin a san cewa, tazarar da ke tsakanin wadannan wurare guda biyu ya kai KM 1239.42, sannan zai dauki kusan awa 1 da mintuna 52 idan za ku yi tafiya ta jirgin sama, amma Annabinmu Muhammadu (SAW) ya kammala ta a cikin ‘yan dakiku kadan.
To, a wani bangare na wannan dare, wato Miraj, Annabi Muhammad (SAW) ya yi tattaki zuwa sama ta 7, kuma a kowace sama ya hadu da Annabawa kamar haka;
Sama ta 1 ta hadu da Adam (AS)
Sama ta 2 ya hadu da Annabi Isa (AS) da Yahaya (AS).
Sama ta 3 ta hadu da Yusuf (AS)
Sama ta 4 ta hadu da Idris (AS)
Sama ta 5 ta hadu da Haruna (AS)
Sama ta 6 ta hadu da Musa (AS)
Sama ta 7 ta hadu da Ibrahim (AS)
Sannan;
Baitul Ma'amur Da Sidrat Al-Muntaha (Inda aka wajabta masa salloli 50, sannan aka rage ta zuwa 5).
Menene Baitul Ma'mur?
Gida ne, wanda yake a sama ta 7, kai tsaye saman dakin Ka'aba (Dakin Allah). Mala'iku suna yin tawafin wannan gida kamar yadda muke yi a kewayen Ka'aba yayin aikin Hajji da Umra. Ka'aba a doron kasa ita ce kwafinsa. Mala'iku 70,000 ne ke ziyartar wannan gida a kullum suna yin addu'o'insu kamar yadda hakan zai ci gaba har zuwa ranar sakamako. (Sahihul Bukhari 3207 da Sahihu Muslim 164).
Menene Sidrat Al-Muntaha?
Itace magaryar tukewa kuma ita ce ƙarshen sama ta bakwai. Ita ce iyakar da babu wanda ya taba wucewa sai Annabinmu (SAW) kuma ita ce wurin da Manzon Allah (SAW) ya yi tafiya tare da Jibrilu, inda Allah ya rage mana salloli daga 50 zuwa 5 bisa rokon Annabi Muhammadu (SAW).
Ita kanta tafiyar da akayi dashi ba tare da ya nema ba. an yita ne domin girmamawa gareshi tare da rarrashinsa bisa abinda mutanensa (Quraishawa) sukayi masa ﷺ. An Turo masa da mafi girman daraja acikin Mala’iku domin ya zama mai rakiya gareshi ﷺ. Wato Mala’ika Jibreelu (Alaihissalam).
An turo masa dabba mafi daraja daga cikin dabbobin gidan Aljannah (Buraaqah) domin ta zamo abin hawansa a wannan tafiyar, har ma dabbar ta nemi cetonsa, kuma ya lamunce mata. (Kamar yadda yake awasu riwayoyin). Kafin su isa Baitul Maqdis, tun tuni har Allah ya tattaro masa dukkan Annabawansa guda 124,000 domin su taryeshi. (wannan ma wata girmamawa ce wacce wani Annabi bai sameta kafinsa ba. ﷺ.
Limancin da yayi ma Dukkan Annabawan Allah (alaihimus salam) Ciki har da Annabi Ibrahim (Ibrahim) Da Annabi Musa (Musa), Da Annabi Isa (Isa bn Maryam). Bayan sunyi sahu-sahu har da Mala’ika Jibreelu alaihis salam. Manyan Manzannin Allah (alaihimus salam) tare da Manyan Mala’ikunsa sun tsatsaya a cikin dukkan sammai domin jiran isowar SHUGABA ﷺ. Ya samu Gaisuwar girmamawa daga dukkan Mala’iku da Annabawan Allah (alaihimus salam).
Limancin sallar da yayi musu a kowacce sama daga cikin sammai bakwai. Ya shiga har cikin Gidan Aljannah, ya zagaya, yayi kallo. yaga ni’imomin dake cikinta. Harma ya bada labari ga al’ummarsa.
Ya shiga cikin wuta ya lekata ya ganta tare da azabar da take kunshe dashi, kuma yaga mazaunan cikinta. Ya gaisa yayi zance na musamman da Manyan Mala’iku irinsu Maliku, Ridhwanu, Israfeel, Mika’il, da kuma Mala’ikan Mutuwa. Yaje magaryar tikewa (Sidratul Muntaha) ya wuce har gaba da nan. An cudanyashi a cikin kogunan haske, Kuma ya keta hijabai yaje inda babu wani wanda ya taba zuwa daga cikin halittar Allah.
Ya hau shimfidar girma, ya kusanta da Ubangijinsa (SWT) irin kusancin da babu irinsa. Ubangijinsa ya girmamashi, yayi zance dashi. Har yau babu wanda ya san zancen da sukayi.
Ubangijinsa ya sanar dashi ilimin halittun farko da halittun karshe, kuma ya kara masa da wani ilimin. (wanda wata halitta bata sanshi ba). Ubangijinsa ya bashi Sallah dashi da al’ummarsa.
An dawo masa da idanuwansa cikin zuciyarsa kuma yaga Ubangijinsa (SWT) kamar yadda yazo a ruwayar Ikrimah daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Abbas (radhiyallahu anhuma) kamar yadda Imam Tabary ya kawo acikin Tafseerin Ayah ta 11 acikin Suratun Najmi). Yaga Mala’ika Jibreelu abisa ainihin siffarsa wacce Allah ya halicceshi a kai tare da fuka-fukansa guda dari shida (600).
Don haka daya daga cikin muhimman darussa na Al-Isra’i wal-Mi’raji, shi ne cewa ‘A kowace wahala (za a samu) sauki’ (k:94:5).