Muhammad Sunusi Lamido Sunusi and Abba Kabir Yusuf |
An aikewa majalisar dokoki takardar neman rushe Masarautu hudu da dawo da Sunusi Sarkin Kano
Yanzu haka wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rushe dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta gabata ta kafa, tare da neman a maido da Sarkin Kano na 14 Mallam Muhammadu Sanusi II.
Bayanin kungiyar na zuwa ne ta cikin wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024, da aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, inda ta ce rusa masarautu tare da maido da Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar Kano.
Jaridar Kadaura24 ta rawaito cewa rubutun wasikar na cewa:
"Mun rubuto wasikar ne don rokon wannan majalisar da ta yi gyara a dokar masarautun jihar kano, muna so a gyara dokar ta yadda za’a rushe sabbin masarautun da aka kirkira guda hudu a shekarun baya."
Wasikar ta ci gaba da cewa, “Mun yi imanin idan har aka hade masarautun suka koma masarauta daya za’a fi samun hadin kai da ci gaban al’ummar Kano”.
“Kuma rushe masarautun gusa hudu zai inganta zaman lafiya da tattalin arzikin jihar kano, don haka muke neman wannan gida zai yi abun da ya da ce dai-dai da doka”.