Yadda Wata Sabuwar Amarya Ta Yanke Azzakarin Mijinta Bayan Da Ta Fara Sumar Da Shi

Yadda Wata Sabuwar Amarya Ta Yanke Azzakarin Mijinta Bayan Da Ta Fara Sumar Da Shi
Yadda Wata Sabuwar Amarya Ta Yanke Azzakarin Mijinta Bayan Da Ta Fara Sumar Da Shi 

Yadda Wata Sabuwar Amarya Ta Yanke Azzakarin Mijinta Bayan Da Ta Fara Sumar Da Shi 


Tunda fari dai amaryar ta bukaci angon nata mai suna Sai'idu da ya siyo mata Madara ne bayan da ya dawo daga wajen sana’anarsa ta saran Itace a Jeji, lamarin da yasa ya je siyar da itacen bai siyu ba, inda ya ranto kudi ya siyo ya kawo mata, dan haka ta bukaci ya rakata bakin Labi ta tsinko ganyen Magani, ashe ta boye Tabarya da wuka a Hijabi.


Suna zuwa bakin labi gurin da babu mutane kawai sai yaji ta kwantare masa Kai da tabaryar ta baya har ta kai ta karya masa Mumamuki ta zubar masa da Hakora ya suma, daga nan akayi zargin ta zaro wukar inda ta yankesu ta saka su a Leda.


Lamarin dai ya faru ne a yakin Karamar Hukumar Kagarko dake jihar Kaduna, inda amaryar mai suna Fiddausi ta yiwa mijinta Sai'idu wannan aika-aikar. 


Bayan da asirinta ya tonu ne aka kai ta wajen ‘yan sanda, inda a yanzu shi kuma yake kwance a Asibitin koyarwa na Mallam Aminu kano, sai dai likitoci sun ce idan ma ya rayu to babu zancen Makarfafar domin yanzu haka ta riga ta rube a ledar har an binne ta.


Shafin Dala-Fm sun rawaito cewa wakilinsu ya samu tattaunawa da ‘yar-uwar angon Zulaihat Muhammad wadda ta ce, auren zumunci aka yi musu, kasancewar iyayen angon mai suna Sa’idu Lawal ‘yan uwan iyayen amaryar ne.


Ta kuma ce yanzu haka amaryar da ake zargin ta na hannun mahukunta a jihar Kaduna, inda al’amarin ya faru a garin Tafa har zuwa aga abun da hali zai yi dangane da jikin angon na ta idan ya rayu, kasancewar kwanaki 12 da yin bikinsu al’amarin ya faru.


Jama'a dai na ta bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin, inda wasu ke kira ga iyaye da su daina yiwa 'ya'yan su auren dole, su kuma maza su daina cewa Sai sun auri macen da bata son su domin yana daga cikin abinda ke jawo faruwar irin wannan al'amari.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post