Yadda Ake Maganin Zafin Nakuda

Yadda Ake Maganin Zafin Nakuda
 Yadda Ake Maganin Zafin Nakuda 


Akwai addu'ar da ake yi idan mace na cikin nakuda don samun Sauki da haihuwa cikin lafiya 


Mata da dama na shan wuya da wahala a lokacin da suke yin nakuda. Hakan yasa tambayoyi suka yi yawa kan neman maganin zafin nakuda. 


Maganin Zafin Nakuda 

Assalamu alaikum, Don Allah Malam a taimaka mana da addu'ar nakuda Don muna hanya ko yau ko gobe Allahu a 'alam. 

Allah yasa kawa Malam da gidan aljannatul firdausi.


 AMSA:

Wa'alaikum assalam, Ban san wata addu'a ta musamman ba wacce Mai nakuda za ta karanta, amma za ta iya karanta addu'o'in da suka tabbata a Sharia ana karantawa saboda tunkude tsanani kamar:


1- اللهم لا سهل إلا ما جعلته سهلا وأنت تجعل الحزن إذا شئت سهلا. 


2. لا إله إلا أنت سبحانك إني كنت من الظالمين. 


3. حسبنا الله ونعم الوكيل. 


Allah ne mafi sani.


29/11/2016.


Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post