Sirrin Yadda Ake Yin Gyaran Fata Don Mata

Sirrin Yadda Ake Yin Gyaran Fata Don Mata
Sirrin Yadda Ake Yin Gyaran Fata Don Mata 


Salo da hanyoyin yadda ake gyaran jiki cikin sauki 


A yau na zo muku da hanyoyin yadda ake gyaran fata, kamar yadda na bayyana muku a shirin mu da ya gabata na hanyoyin gyaran jiki, yau na kawo muku hanyoyi da za ku iya gyara fata ta yi kyau musamman ga matan dake shirin yin aure. 


Ga jerin hanyoyin Yadda Ake yin gyaran fata kamar haka;


Gyaran Fata Na Daya (MAI DA TSOHUWA YARINYA)

Wannan hadin shima hadine na musamman wanda yakesa fatar mace ta zamo tana tare da shauki da laushi, kai harma taji jikinta yana wani damshi-damshi. Samu wadannan abubuwa don yin hadin;

 • Lemon tsami
 • Madarar shanu ko peak milk"
 • Kwai guda 3
 • Ayaba 

Ki samu ayaba mai kyau ki bare ko ki matse da hannunki, ko ki markada yayi laushi. Sai ki zuba tatacciyar madara ki fasa kwai kamar guda uku, amma farin zaki zuba, sai ki matse lemon tsami ki gauraye shi ki shafa ajikinki, ya samu kamar tsawon awa daya, sai kiyi wanka da ruwan zafi.


Idan kika lazimci yin haka kamar kwana uku zakisha mamaki. Domin wannan hadin mata da yawa suna amfani dashi kuma suna ganin amfaninsa. 


Gyaran Fata Na Biyu -(MAI LAUNI) 

Shima wannan hadin yana da muhimmanci sosai domin kuwa yana gyara fata sosai, nemi wannan abubuwan kamar haka;

 • Lemon tsami
 • Bawon kwai
 • Kurkur

Zaki hadesu guri guda ki daka su sai ki rinka wanka dashi. Fatar mace zata goge tayi kyawun gaske.


Gyaran Fata Na Uku 3 (LU'U-LU'U)

Hadi ne na musamman wanda yake kama da 'maida tsohuwa yarinya', kina iya samun wadannan abubuwan kamar haka;

 • Sabulun salo
 • Man auduga
 • Dudu osun
 • Dettol
 • Lemon tsami

Zaki hade su guri guda ki rinka wanka dashi. Fatarki zatayi laushi da santsi.


Gyaran Fata Na Hudu (ZINARIYA)

Wannan hadin gyaran fata ne da ake kira da zinariya, domin yana taimakawa wajen kara gyara fata tai kyau da haske, nemi wannan abubuwan;

 • Ganyen magarya
 • Sabulun salo

Zaki daka ganyen magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka. Yana gyara jiki sosai. 


Gyaran Fata Na Biyar (MAI LAUNI)

Shi kuma wannan ana yi masa lakabi da mai launi, ki samu wannan abubuwan kamar haka;

 • Ganyen magarya
 • Man alaiyadi
 • Man habbatus sauda

Zaki daka ganyen magarya a zuba acikin man alaiyadi da hahbatus sauda. Shima yana gyara jiki.


Gyaran Fata Na Shida 6 (MAI TASA)

Shi kuma wannan an yi masa lakabi da mai tasa don kuwa yana gyara fata sosai, ki samu wannan abubuwan kamar haka;

 • Lalle
 • Garin ridi

Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka, sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki dashi. Zuwa awa daya, sai kiyi wanka.


Gyaran Fata Na Bakwai (BATA TSUFA)

Wannan yana da matukar kyau, don yana gyara fata ta yi kyau sosai. Ana yinsa da wadannan abubuwan;

 • Man zaitun
 • Ridi

Zaki daka ridi, amma sai kin gyara shi kin shanya ya bushe, sai ki daka ki zuba cikin man zaitun. Idan zaki kwanta bacci sai ki shafe fuskarki da jikin ki, da safe ki wanke zaki sha mamaki.


Wannan sune hanyoyin gyaran fata da mata za su dinga yin amfani dasu, Indai kika rike wasu daga cikin wadannan hanyoyin da na kawo muku babu shakka za ku samu biyan bukata. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post