Siffofin Tantanin Budurci Mata

Siffofin Tantanin Budurci Mata
Siffofin Tantanin Budurci Mata 


Tantanin Budurci, wata 'yar fata ce ko kuma raga da take toshe da kofar Farji ta kasa daga waje


Tantanin Budurci a jikin mace, wata hikimace ta Allah (S.W.T) a fili karara domin kuwa ya sanya wannan tantani ya zama wani matoshi ko makari da zai hana bazuwar jima'i Barkatai, ba tare da tsari ba Wanda hakan daga karshe ka iya wargaza rayuwar al'umma, musamman rayuwar Mata.


Shidai Budurci haryanzu yana da sauran darajarsa domin kuwa a wasu 'yan lokuta idan Ango ya sadu da Amaryarsa ya samu cewa ba Budurwa ba ce, wannan ya kansa ya sake ta ko kuma mutuncinta ya zube daga idanun sa. Domin maza da yawa na zargin idan ba su ne suka fara kwanciya da mace ba babu yadda Za'a yi ta rasa budurcinta. 


Siffofin Tantanin Budurci 

Tantanin Budurci, wata 'yar fata ce ko kuma raga da take toshe da kofar Farji ta kasa daga waje, kuma dumbarun farji suna kange da ita. Kamar yadda mukai bayanin yadda nau'in budurcin mace yake a darasin mu na baya, kuna iya latsa nan


Shi dai siffofin tantani suna bambanta ne daga wasu matan zuwa wasu Mata, amma wanda yafı yawa a tsakanin 'yan mata, shine wanda yake da wata huda huda kewayayya a tsakiyarsa, wadda girman wannan huji yasha bamban a tsakanin Mata.


Sai kuma mai kamar Wata a farkon kamawarsa har zuwa yayi kwana biyar, wannan kuma kofar da take tsakiyarsa kamar Wata take.


Sannan kuma akwai tantanin dake da siffar Mai raga-raga, wannan shi kuma kananan kofofi da dama ke kare shi kamar dai yanda raga take.


Wannan sune yadda siffofin tantanin budurci mace yake, akwai bayani masu ilimantarwa idan kuka Karanta abubuwan da mukai tun daga darasin farko, da fatan kun ilimantu. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post