Sabon labari: Kotun shari'ar Muslunci a Kano ta yanke hukunci ga Murja Ibrahim Kunya

kotun tayi umarni da a Mika Murja Kunya asibiti domin yi mata gwajin kwakwalwa.
Murja Ibrahim Kunya 


kotun tayi umarni da a Mika Murja Kunya asibiti domin yi mata gwajin kwakwalwa


Bayan cece-Kuce da al'umma ke yi kan fitar da Murja Kunya daga gidan gyaran hali, a ranar Talata 20/2/2024 kotun shari'ar musulunci bayyana matsayarta kan hukuncin da za'a yi wa Murja anan gaba. 


Kotun shari'ar musulinci ta jihar Kano karkashen jagorancin Mai shari'a Nura Yusuf ta sanya ranar 20 ga watan 5 na wannan shekarar da muke cikin domin cigaba da sauraran karar da aka shigar gabanta ta jarumar TikTok da aka fi sani da murja kunya.


Sai dai kafin sannan kotun tayi umarni da a Mika Murja Kunya asibiti domin yi mata gwajin kwakwalwa.


Wannan yana nuna jarumar Tiktok za ta ci gaba da zama a gidan gyaran hali har nan da wata 3 masu zuwa. 


Shin yaya kuke ganin wannan matakin da kotun shari'ar musulunci ta yanke kan Murja Ibrahim Kunya?


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post