Lokuta, Wuraren Da Halayen Da Ake Karbar Addu'a

Lokuta, Wuraren Da Halayen Da Ake Karbar Addu'a

Lokutan Da Ake Karbar Addu'a

Lokutan Da Ake Karbar Addu'a

Malamai sun bayyana lokuta da wurare da kuma halayen da ake karbar addu'a musulmi. Ina fatan duk wanda ya Karanta wannan rubutun zai taimaka ya turawa sauran yan uwa Musulmi. 


Lokutan Karbar Addu'a 

 1. Daren lailatul qadr
 2. Yankin dare na karshe
 3. Gurbin sallolin farilla
 4. Tsakanin kiran sallah da iqama
 5. Wata sa'a cikin kowane dare
 6. Lokacin saukar ruwan sama
 7. Lokacin da akeyin sahu don fita yaki domin Allah
 8. Wata sa'a cikin ranar juma'a. Ana rinjayar da wannan sa'ar da cewa daga sallar juma'a ne har zuwa bayan sallar la'asar.
 9. Lokacin shan ruwan zam-zam
 10. Yayin da ake yin sujada
 11. Lokacin farkawa daga bacci idan akayi addu'a
 12. Lokacin da ake yin addu'a kamar haka;" لا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ""La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin".


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post