Amfanin Shan Danyen Kwai Ga Mace

Amfanin Shan Danyen Kwai Ga Mace
amfanin kwai ga mata


Amfanin kwai ga mata yana magance kurajen fuska duk wani pimples na fuska yana konewa 


Kamar yadda a darasin mu na baya muka kawo muku amfanin shan danyen kwai ga maza, yau kuma za mu Karkata bayani kan amfanin kwai ga mata. Da fatan za ku amfana daga abubuwan da za ku Karanta. 


Amfanin Shan Kwai Ga Mata

Amfanin kwai ga mace yana da yawa sosai kamar yadda muka kawo muku a darasin mu da ya gabata, shi kwai na dauke da sinadarin minnerals, carbohydrates da protein wanda ke taimakawa garkuwar jiki, karfin ido da sauransu. Amfani kwai ga mata yana da yawa, amma ga wasu daga cikin su kamar haka;


Amfanin Danyen Kwai 

1- Ruwan kwai nada sinadarin gina jiki, da kuma sinadaran Bitamin wanda ke taimakawa jikin mace kara samun lafiya. 


2- Ruwan kwai na rage tsufar fuska, ansan  mata da son gyara jiki da son kwalliya, yin amfani da danyen kwai ga mata na taimaka musu kara kyau da lafiyar fuska. 


3- Danyen kwai na kare fuska daga yawaitan fitar kuraje, amfanin kwai ga mata yana magance kurajen fuska duk wani pimples na fuska yana konewa idan ana amfani da danyen kwai. 


4- Danyen kwai na kara ma fuska haske, bayan kawar da kurajen fuska danyen kwai na kara haske da cire dukkan dattin dake dankare a fuska. 


5- Ruwan danyen kwai na rage kumburin idanu, sannan yana kara lafiyar idanu kamar yadda na fada tun a farko. 


Yadda Ake Hadin Danyen Kwai

Yadda ake hada ruwan kwai don samun bukata shine, za'a fara turara fuska da ruwan zafı, sannan abi da Rose water a shafe fuskar, kamar yadda majiyar mu ta ruwaito.


Daga nan sai a fasa kwai, a cire kwanduwar, sai a kada farin ruwan kwan, har sai yayi kumfa, bayan nan sai a shafe fuska da wannan ruwan kwai, sai kuma a daure fuskar da takardar 'Tissue' a manna a fuskar, a kara samun takardar a sake mannawa a dukkanin fuskar.


Da zarar fuskar ta bushe a haka, sai a wanke fuskar, sannan a shafe fuskar da kwanduwar ita ma, sa'annan a wanke, idan an cigaba da wannan tsari, za'a samu biyan bukata.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post