Alamomin Mace Idan Batasan Namiji

Alamomin Mace Idan Batasan Namiji
Alamomin Mace Idan Batasan Namiji 


Alamomin Da Zaka Gane Mace Bata Sonka 


Idan mace bata son namji akwai wasu dabi'u da take yi wanda za kai saurin ganewa, sai dai maza da yawa basa gane alamomin da mace ke yi idan bata son su. Hakan yasa muka kawo muku wasu daga cikin alamomi na zahiri da za ku fuskanta. 


Alamomin Mace Batasan Namiji 

Wasu daga cikin alamomin da zasu tai makama ka gane budurwa bata Sonka sune kamar haka;

1) za ka ga sau da yawa kana hira da ita bata sakewa tayi hira, sai dai kaji tana um, eh, a a, to, to ya zance ma, kuma ba wai rana daya ba, ba kuma laifi kaimata ba, kuma kasan ita me surutuce ba wai kunyaceba a ranaku da yawa idan kuna zance haka take yima.

2) wata zata dinga yawan tunani, a lokacin da kuke hira inkai magana tace ina ji ba kace kaza da kaza ba ta dan fadi 2/5 na abun da kace tai shuru.

3) kallon raini a fakaice, ko a dan fake ka a harareka :

4) Idan ka tura a kirata bata fitowa da wuri kuma ba ace ma tana wani abunba kamar cin abunci wanka, kwalliya da sauransu, kuma intazo bakaga alamar sabuwar kwalliya ba, kuma batace ma, masoyi kayi haquri na batama lokaci, kaza da ka nakeyi. kuma kullun hakatake ma.

5) Bata fıya yin kwalliya in kazo ko a yaya ta fito, watama saita munanta kanta zata fito dan kace baka SO :

6) In matan gidansu ko kawayenta suna hirarka suna fadar kirkinka ita zata dinga jin haushi, ko ta tashi daga gun ko takama zumbura baki ko hararar me fadar, wani Iokacin har da fadar bakar magana.

7) Bata fiya damuwa da ta kiraka a waya ba, koda pls cal me ko flashing, sai dai intana da wata buqatar take da ita ta daban. Wannan ma shine yafı bakantamin rai.

8) idan daukar wayanka dawuri kuma koda tana kusa, kuma kusan kullum, sannan bata fadama dalili ba ko dadadan kalamai balle tanemi afuwarka.

9) Idan ka bata abu bata nuna farinciki balle godiya, ko taki karba tana me masa yanga

10) Bata fıya kula yan uwanka ko kannanka koda a waya ne ta tambayi lafıyarsu

11) wata tana iya zagin kama a bayan idonka ko ta canjama suna misali, wawana, da dai sauransu

12) In tatashi fitowa gunka zance zata zo ranta a bace, batare da ta fadama dallin bata rantaba

13) Intafito wata har tsaiwarta ma zakaga kamar zakuyi fada da ita

14) In kanemi kaje gidan su ko ka ai ko magabatan ka bata yadda, kuma batare da wani dalili me qarfı da ta fadama akan hakan ba.


Wannan sune alamomin mace batasan namiji, idan kana tare da budurwarka daga yau ka fara duban wadannan alamomin idan ka fuskanci tana yi maka wasu daga cikin wadannan sai kasan matakin da Zaka dauka.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post