Abubuwan dake sa mace taso namiji

Abubuwan dake sa mace taso namiji
 Abubuwan dake sa mace taso namiji 


"Ni ban son wahala, ban son auren talaka, ina son auren namiji mai kudi wanda zan huta in samu kwanciyar hankali, auren talaka ai musiba ne"


Shin kokasan cewa da akwai abubuwan da ke sa mace taso namiji? Wanne kasani daga ciki? Idan baka sani ba na shirya kawo muku su. 


Kamar yadda maza ke da abubuwan da ke sa su so mace, haka suma mata kowacce tanada irin nata abubuwan dake sa ta kamu da so da kaunar namiji. Kowace mace na da irin zabin ta, wata kyau take dubawa, wata kuma nasaba, wata kuwa ado da iya kwalliya ne ke jan hankalin ta. 


Abubuwan dake sa mace taso namiji

Na yi tattaunawar jin ra'ayoyin wasu mata kan irin zabin namijin da suke so wanda kowace ta bayyana irin nata ra'ayin da ya bambanta da na sauran. Gasu kamar haka;


1) Tsafta, Fatima Ibrahim ta ce ita babban abinda ke birge ta da namji har ta ji tana son sa shine tsafta. Duk irin munin da namji ke dashi Indai yana da tsafta kuma ya iya wanka da saka kaya ita shi take so. Ni namji mai kyau baya birgeni Indai bai da tsafta, cewar Fati. 


2) Kudi, Maryam Kabir kuwa cewa tai gaskiya ita abubuwan dake sa taso namji kudinsa, "ni ban son wahala, ban son auren talaka, ina son auren namiji mai kudi wanda zan huta in samu kwanciyar hankali, auren talaka ai musiba ne", a cewar ta. 


3) Kyau, ni ba mai kyau bace, kuma ba mummuna bace amma ina son samun namiji mai kyau wanda za mu haifi yara kyawawa, Inji Amina Umar. Ta ce bata son ta auri namijin da ta fishi kyau don za su yi ta haifar yara munana. 


4) Asali, ita kuwa Ilham Kamal cewa tai auren maza a yanzu sai a hankali, don sai ki auri namiji yazo yana yi miki rashin mutunci. Amma samun namiji dan asali masu mutunci sun fi rike mace da kima da mutunci. 


5) Mai Ilimi, Khadija Mohd kuwa cewa tai ita babban abubuwan dake sa ta so namji shine Ilimi, burina na samu mai ilimin addini da boko. Wanda 'ya'yana za su yi alfahari dashi. 


Wannan sune wasu daga cikin tarin ra'ayoyin mata kan zabin su ga namji, da abubuwan dake sa mace taso namiji. Shin ke ma da kika Karanta wannan ra'ayoyin, kina da naki da za ki iya bayyana mana? 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post