Abu 3 Dake Jan hankalin Mace Ga Namiji

Abu 3 Dake Jan hankalin Mace Ga Namiji
Abu 3 Dake Jan hankalin Mace Ga Namiji


Muhimman Abubuwa 3 Dake Daukar Hankalin Mace Ta Ji Ta Kamu Da Soyayyar Namiji 


Menene ainihin abinda mata suke so ga namiji? Wannan itace tambayoyin da maza ke yiwa kansu tsawon shekaru, kuma babu wata cikakkiyar amsa kai tsaye. Domin mata ba wai abu 1 ne ke jan hankalin ga namiji ba, abubuwa da dama na sa mace ta ji tana son namji. A wannan darasi na yau, zan kawo muku abubuwa 3 da suka fi daukar hankalin mace taji ta kamu da son namiji kamar yadda wani bincike ya tabbatar. 


1) Kyau (Handsome); da yawa daga cikin mata na son namiji don kyaun halittar da Allah yai masa. Mata suna son haifar yara masu kyau, koda mace bata da kyau, amma tana son ta samu namiji mai kyau wanda idan ta haihu 'ya'yan su yi kamannin sa. 


2) Kudi (financial); A Wannan zamanin idan zaka ware mata 100 zaka samu kaso 90 na son auren namiji mai kudi. Kowace mace burinta ta auri mai kudi don ta samu hutu da biyan bukatun rayuwa na yau da kullum. Duk irin munin namji a wannan zamanin Indai yana da kudi za ka ga yana iya auren mace duk irin kyaun halittar ta. 


3) Mai Kirki (Kindness); Samun mutumin kirki shine abu na 3 dake jan hankalin mace ga namji, samun namji mai kirki mai mutunci da mutun ta mace da iyayenta da yan uwanta shine burin duk wata mace. Mace duk rashin kirkinta da rashin mutuncin ta tana son ta samu ko auren namji mai kirki. Domin an san namji mai kirki da tausayi, da jin-kai. 


Akwai abubuwa da dama dake jawo mace ta kamu da son namji, sai dai ba za mu samu damar kawo muku su duka ba a yau. Nan gaba za ku ji mu da abubuwan da ke jawo hankalin namji ga mace. Sannan kuna iya bayyana mana ra'ayoyin ku a sashin sharhi.

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post