Yanda Ake Dafa Kazar Amarya

Yanda Ake Dafa Kazar Amarya
Kazar Amarya 


Shin a matsayinki na amarya kinsan yadda ake dafa kazar amarya? Ga wani sabon hadi mai muhimmanci 


Tsarin da mata da yawa suke bi wajen dafa kazar amare da yawa kuskurene kuma sihirine. Wannan shine dalilin da yasa koda a littafin DAKIN AMARYA ba'a kawo bayaninba saboda mata da yawa ba zasu dauki wanda aka yi ba. 


Kuskurene a ce sai an zuba rubutun ayoyin Al-qur'ani a ciki ko kuma ace mace daya ita za ta ci wannan kazar ko kuma ace dole sai ranar laraba duk wadannan ba sune sukesa namiji ya makalewa maceba kuma ita wannan kazar anayinta saboda tana tabbatarda ni'ima a jikin mace sannan gaban mace ya ciko kuma tana saka mace tayi dandano sosai ta yanda mijinta kowanne lokaci zaiso ya sadu da ita haka kuma tana saka mace ta zama me sha awa amma maganar mallakar miji wannan ba gaskiya bane.


Yanda Ake Dafa Kazar Amarya 

Ta yaya ake dafa kazar amarya? Ku Karanta da kyau sanni kuma ku jarraba. 


ki samu ridi danye ki dakashi ya zama gari saiki samu harzar kabewa ki zuba mata ruwan zafi ki barta ta jiku, sai ki tace ruwan sannan sai ki zuba wannan garin ridin sannan Ki daka minannas ki zuba garinsa aciki to wannan ruwan shine zaki dafa kazar a ciki. 


Amma ki samu budurwar kaza bayan kin gyarata kin cire kayan hadin saiki zuba idan da hali ki samu farin gadali ki daka ki zuba aciki zaki iya zuba kayan miya yanda kikeso ki dafata ta dafu sosai sannan ki sauke ki cinyeta gaba daya har miyar. Wannan itace kazar amare kuma kowacce mace zata iya kuma zatayi idan saura kwana hudu a sadu da ita.


Wannan shine yanda ake dafa kazar amarya, duk matan aure suna iya yin wannan hadin ba sai amarya ba domin kuwa hadin yana taimakawa mace wajen Karin ni'ima wajen mijinta. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post