Yadda Ake Gane Inzali Mace (zuwan kai)

Yadda Ake Gane Inzali Mace (zuwan kai)
Ya ake gane inzalin mace yake


 Masana sun yi bayani ya ake gane inzalin mace a lokacin da ake yin Jima'i 


Maza da yawa na neman a yi musu bayani akan yadda mata suke zuwan kai ina nufin inzali. Domin akwai wani miji da yace Kusan watannin 8 kenan da yin aurensa amma ko sau daya bai taba ganin ta kawo ba kamar yadda yake yi. kuma idan yana kallon bidiyo na baɗala yana ganin yadda mata ke zuwan kai kamar yadda maza keyi. Ko dai matata ce batada lafiya?

To ba shi kaɗai bane, maza magidanta masu shekaru ma suna da jahilcin zuwan kan mata. Mun sha samun tambayoyi akan wannan lamari daga wajen maza da mata.

Kai harma wasu mazan da suka saki matansu saboda wai basa kawowa. To Ƙara natsuwa ka fahimci yadda abun yake.

 

Yadda Ake Gane Inzali Mace

Inzalin mata ba kamar yadda na maza yake bane. Su maza suna fitowa da maniyi ne a zahiri yadda ana iya ganin sa amma inzalin mata shi a kwakwaluwansu yake don haka internal enjaculation suke yi ba external ba. Sai dai akwai wasu matan da suna iya ɗigar da ruwan miniyinsu amma ba kamar yadda na maza ke fitowa ba.

Gane inzalin mace ba abune mai sauki ba, Shi ruwan maniyin mace yana nan kamar ruwan maziyin namiji ne bashi da kauri, tsinkakke ne kuma fari, amma na maza kamar majina yake.

A kwanakin baya mun yi darasi akan mata masu feshi, matan da suke fesar da ruwa mai kama da fitsari wanda maza da yawa suna ɗaukar cewa wannan shine inzalin mace. Kuma shine na tabbata wasu ke tunanin inda muka tabbatar da cewa inzalin mace daban shi kuma wannan ruwan yana samuwa ne a lokacin da mace ta gurzu take cikin jindaɗin jima'i.

Inzali ga maza da mata shine ƙololuwar jin daɗi a lokacin jima'i. A lokacin da mace ta kamu da shauƙin jima'i, wannan lokacin jinin jikinta yake kwarara zuwa kan ɗan tsakanta, daga bisani sai ruwan maniyinta dake tare a mafitsaranta ya bazu zuwa sassan jikinta har kwakwaluwanta a lokacin da zata yi zuwan kai.

Akasarin mata basa fitar da maniyi idan sunyi inzali. Amma da akwai alamomin da namiji zai iya fahimtar matarsa ta yi zuwan kan. 


Ga Wasu Daga Alamomin Inzalin Mace

1) Wata matar idan ta yi inzali tana ƙanƙame jikin mijinta tare da yin nishi mai ƙarfin gaske wanda yake nuna alamar ta yi inzali.

2) Wasu matan idan za su yi inzali za kaji suna yin surutu da sumbatu iri-iri, idan kana yin jimai da mace kaji tana irin wannan yanayin alama ne dake nuna ta yi inzali 

3) Wasu matan kuma kuka suke yi sosai a yayin da suke yin inzali, amma irin kukan jindaɗi ne wanda ke nuna sun samu gamsuwa.

Waɗannan sune wasu daga cikin alamomin inzalin mace a lokacin da take yin zuwan kai. Kowace mace da irin salon yadda take yi idan za ta yi inzali, mazan da suke cewa matansu basa yin inzali ku sani cewa mata basa fitar da maniyi irin yadda maza suke yi. Da fatan kun ilimantu, Allah yasa mu dace.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post