Suffofin Wankan Tsarki

Suffofin Wankan Tsarki
Suffofin Wankan Tsarki 


Suffofin yadda ake yin Wankan Tsarki 


Na ambaci tsarki ne don faɗaɗawa, amma da wankan janaba, dana haila, ko juma'at dana jinin biki duk suffar iri daya ce kurum niyya ce ta bambanta.


Amma bari mu yi bayani na janaba a aikace don shine aka fi yi akai-akai, 


Tashin farko Bayan ka debi ruwanka a robar wanka ko bokiti mai tsarki da tsarkakewa ka kai bandaki. Sai kayi waɗannan abubuwa:


1- Farawa da karkato bakin robar ko amfani da kofi ka debo ruwa ka wanke hannuwanka kafin fara wankan.


2- Sai ka ɗaura niyyar wankan (Nawaitul gusulul janabati) basai ka furta ba amma aranka zaka kudurce hakan. 


3- Sai ka tsarkake Al'aura tare da istinja'i matsowa ahankali ka wanke abinda ya makale na (Maniyyi) daga kororon mafitsara. Zaka wanke sau uku ko abinda ya sauwaka ka tabbatar dai ya wanku


4. Sai yin Alwala irin yadda akeyinta idan za ai Sallah wato har zuwa shafar kai. Toh saide bambancinta da alawar sallah shine a iya shafar kai zaka tsaya ba zaka wanke Kafafuwanka ba tukun. 


5. Daga nan bayan shafar kai saika sa yatsun ka duddurza gashinka kamar wanda za'ai ma aski da aska. Saika debo ruwa da hannunka ka wanke kan sau uku, tare da tabbatarwa ruwan ya shiga ko ina, har ƙarƙashin gashin kai musamman a Mata saboda gashinsu nada tudu da yawa.


6. Saika tsaga jikinka biyu ka rika Zuba Ruwa kana cudawa a bangaren Jikinka na Dama tunda tsakiyar kanka har zuwa fuskarka, wuyanka, kafadarka, hannun dama, kirji, ciki, mara, cinyar kafa zuwa karshen yatsun kafar na dama. Wato tsagin jikin dama kasan a alwala baka wanke kafafu ba toh anan ne idan ka gangaro zaka wanke kafafun


7. Bayan gamawa da bangaren dama saika kuma zubo ruwa daga tsakiyar kan har zuwa kafafunka da yatsun kafar. 


Kaga daga nan zai zamto ko ina na jikinka ya sami ruwa shikenan ka idar da wankan janaba na SUFFATUL KAMALAH


Siffar yadda ake wanka swimming pool da shower 

Idan Kuma Swimming Pool Ne Ko Kuma Shower 

Malamai sunce a irin wannan yanayin abinyi kurum shine: kai tsarki saika kudurci niyyar wankan da zakai saika afka cikin swimming pool ɗin shikenan, idan ka tabbatar ka jiku ko ina na jikinka ya taɓi ruwa saika fito ka daura alwala kamar yadda akeyin ta sallah amma a wannan alawar ita har kafafu zaka wanke complete... Shikenan wankan janaba ya kammala. 


Haka ma in shower ce, bayan ka yi tsarki saika kunna ka saki ruwan baki daya duk jikin. Idan ka gama sai kai alwala shikenan. (Suffatul ijzah kenan) 


Kada A Manta Abubuwan Dake Haddasa Wankan Janaba Sune kamar haka:


1. Idan anyi mafarkin saduwa da Mace Ko, Namiji sai anyi wanka har ya zamto da aka farka anga maniyyi a tufafi toh koda ba a iya tuna mafarkin ba sai anyi wanka


2. Idan an sadu da Mace sai anyi wankan janaba Koda ta hanyar zina ne kuwa. 


3. Haka koda goge akaiwa Macen ajikin al'aurarta matukar maniyyi ya fita ko kuwa kan kaciyar namiji ya buya acikin farjin Mace toh koda ba'ai inzali ankawo maniyyi ba wanka ya kama mutum


4. Hakama masturbation na wajabta wankan janaba. Niyyar wanka a Zuciya ake kudurtawa ana iya yinta tun kafin ma ashiga bandakin basai anfurta ba. Wallahu a'alam.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post