Masu Garkuwa Da Mutane Sun Kashe Dalibar Jami'ar Bayero Saboda Gaza Biyan Kudin Fansa

Masu Garkuwa Da Mutane Sun Kashe Dalibar Jami'ar Bayero Saboda Gaza Biyan Kudin Fansa
Talatu Salihu


Sun kashe ta saboda iyayenta ba su iya biya kudin da suka buƙata ba


Masu satar mutane sun kashe daliba ta Jami'ar Bayero, Kano (BUK), mai suna Talatu Salihu, masu garkuwar sun bayyana cewa iyayenta ba su iya kawo kudin da suka buƙaci abasu ba don su sake ta.


Talatu Salihu, dalibar tana shekara ta ƙarshe a Jami'ar Bayero, Kano (BUK), masu satar mutane sun kashe ta da bayan da suka sace ta tare da yan uwanta a gidansu a Abuja, babban birnin Najeriya.


Talatu daliba ce dake fannin Library and Information Science kuma an kashe ta bayan iyayenta ba su iya biya kudin da masu satar mutane suka buƙaci ba.


Abokai na kusa da Talatu a makaranta sun tabbatar da mutuwar ta ga SaharaReporters a ranar Laraba.


"An sace ta tare da yan uwansa biyu a Abuja kuma masu satar mutane suka buƙaci kudi fiye da miliyan 100 a matsayin kudin fansa wanda iyayenta suka gaza biya. 


"Sun kashe ta saboda iyayenta ba su iya biya kudin da suka buƙata ba," Kawar Talatu ta sanarwa da SaharaReporters.


Ta ce masu satar mutane sun ci gaba da rike yan uwanta da akai garkuwa dasu wanda sukai barazanar cewa idan ba'a biyasu kudin da suka nema ba za su kashe su. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post