Manyan Alamomin Balagar Mace

Manyan Alamomin Balagar Mace
Alamomin Balagar Mace


Manyan Alamomin Da Ake Gane Balagar Mace


Balaga wani yanayine dake faruwa da mace a lokacin da takai shekara 8 zuwa 13 Shine lokacin da jikin zai karasa girma wanda ke nuna ya kai ga zai iya daukan ciki da kuma haihuwa.


Kusan kowace mace da irin yanayin yadda balaga ke zuwa mata, wata alamomin bayyanar balagar suna bayyana da wuri wasu kuma ba da wuriba. Wani bincike ya bayyana wata macen tana iya fara balaga daga shekara 7 amma babu sahihanci akan hakan, wanda yafi tabbas shine daga shekara 9 ne wasu ke fara nuna alamun balaga.


Alamomin balaga ya mace

Kamar yadda na fada tun farko Ita dai balaga wani yanayine dake faruwa da mata da zarar sun kai shekarun bayyanarta, hakan yana faruwa ne idan mace ta fara yin jinin al'ada wanda shine alama da tafi bayyana balagar mace.


Manyan Alamomin Balaga Ga Mata

Wadannan sune alamomin da mace Zata gane ko iyaye su fahimci  balagarta ta fara, don haka za ta iya daukan ciki matukar namiji ya kusanceta da jimai. Alamomin balagar sune kamar haka;

1. Fara jinin Al’ada ga mace, shine babbar alama ta farko dake bayyana balagar mace domin idan ta fara jini tana iya daukar ciki Idan an sadu da ita

2. Fitar gashin mara, fitar gashin gaba yana daga cikin alamar balagar mace da za'a iya ganewa.

3. Fitar gashin hamata, ba kowace mace ke fitar da gashin hammata a Karon farko ba

4. Bayyanar majinar farji, fitar wani farin ruwa kamar majina alamu ne dake nuna balagar mace.

5. Fitar kurajen fuska, shima wanna alama ne amma ba kowace mace ke yinsu ba.

6. Fitar nono, na daga cikin manyan alamomin balagar mace da ake gani a zahiri, kai da kaga mace da nono kasan ta balaga.

7. Canjin murya ta koma babba, muryar mace tana sauyawa ta kara kauri da girma a yayin da ta balaga, da sauran wasu alamomi

Wanan sune manyan alamomin da ake gane bayyanar balagar mace, kuma wannan shine yake nuna mace ta isa aure zata iya kwanciya da namiji har ta samu ciki. Idan iyaye sun ga ya'yan sun nuna alamomin balaga sai su yi gaggawar daukar nauyin kara kulawa dasu yadda ya kamata.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post