Maganin karin kiba a sati daya

Maganin karin kiba a sati daya
Maganin karin kiba a sati daya


Hanyoyin da za'a kara kiba cikin sauki a sati daya 


Maganin Karin Kiba Maza Da Mata; kwanciyar hankali da nutsuwa tareda kulawar miji sune kan gaba wajen saka mace murmurewa tayi kyau amma kuma akwai hanyoyi biyu dana kawo a kwanakin baya, kuma jama'a sunyi cikin ikon allah anyi nasara sunzo sunyi godiya saboda haka idan baki ganiba karanta yanzu:


Akwai hanyoyi da dama da ake yin amfani dasu don Karin kiba, sai dai ba kowane ne yake yi yadda ya dace ba, akwai kuma wadanda yin amfani dasu yana da illa ga lafiya. Amma wannan da muka zo muku dasu masu inganci ne. Ga hanyoyin kamar haka;


Maganin karin kiba a sati daya

(1) kisamu yayan hulba ki tafasasu har sai ruwan ya canja, sai ki tace ruwan ki zuba masa Zuma farar saka da madara peak da born vita ki ajiye a cikin fırji, da safe kafın kici abinci sai kisha kafın mako biyu zakiga abun mamaki.


(2) Ita kuma hanya ta biyu waken suya, alkama, gyada, tare da aya zaki samu anaso kiyi garinsu sai ki damasu kamar koko ki zuba madara peak kina sha wannan shima nabaki mako Biyu zakiga kin canja. 


Maganin Karin Kiba

Barkanmu da wanna lokaci sauda dama mutane kan bukaci magani da zai rage musu kiba, amma a wani bangare da ban kuma mutanan suke neman kibar ido rufe.


Muna samun sakonni da dama kan maganin karin kiba, musamman daga yan uwa mata don haka yau shafın yayi bincikensa ya biyo ta bangaren Maganin Karin Kiba.


Ina fata za'a karanta wannan darasi a nutse kuma a turawa yan uwa da abokan arzuka ta kafar WhatsApp ko Facebook.


Abubuwan da zaku bukata don maganin karin kiba sune kamar haka;


Waken soya cokali 2.

Ridi cokali 2.

Dabino cokali 1

Hulba cokali 1

Gyada dai dai misali.

Madarar gari cokali 5


Yadda za'a hada maganin karin kiba a sati daya 

Da farko ku samu waken suya mai kyau (Ku gyarashi sosai a fitar da tsakuwar jikinsa) sai ku soyashi har sai ya fara kamshi, sai ku sauke shi, bayan yayi sanyi sai ku dakashi sosai ya zama gari.


Haka zalika ku samu ridi mai kyau (Ku gyarshi yadda zai zama babu wani datti a ciki) shima sai ku soyashi yadda ya kamata sai ku sauke bayan yayi sanyi sai ku dakashi ya zama Gari.


Haka zaku samu dabino dinku bushashe mai kyau shima ku dakashi yazama Gari.


Gyada kuwa saiku hada kunun Gyada da ita, bayan kun gama sai ku dinga diban wadancen abubuwa da muka lissafa kuna sawa a cikin kunun gyada din kuna sha kullum har tsawon sati biyu zuwa uku insha Allahu zaa baki labarin kibar da kika kara.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post