Ki Guji Yin Wadannan Dabi'un Ga Namijin Dake Son Aurenki

Ki Guji Yin Wadannan Dabi'un Ga Namijin Dake Son Aurenki
Ki Guji Yin Wadannan Dabi'un Ga Namijin Dake Son Aurenki


Ki Guji Yin Wadannan Dabi'un Ga Namijin Dake Son Aurenki


Idan har kin tabbatar namijin da kuke yin soyayya dashi aurenki zai yi, ki tabbatar kin guji yi masa wadannan abubuwan da za mu bayyana muku. Ga abubuwan kamar haka ;


1: Daura Masa nauyin bukatunki Dana gidanku. Kada ki kuskura ki dinga daura masa nauyin ki balle kuma na gidanku. 

2: Yawan rokonsa. Roko yana zubar da kimar mutum, duk irin son da namiji yake yi miki Kada ki dinga rokonsa domin raini zai shiga tsakanin ku. 

3: Ziyarar inda yake zama. A matsayinki na mace Kada ki dauki kafa kije wajen namiji idan baku yi aure ba. 

4: Nuna masa zakuwarki akan aurensa. Ita mace ansanta da class, Kada ki nuna masa damuwar ki kan auren ku 

5: Neman ya rika fita dake yawo. Duk macen dake yin hakan akwai rashin kamun kai a tattare da ita. Ko da wasa Kada ki nemi namiji ya dinga fita dake yawo koda ya nemi yin hakan. 

6: Amsa gayyatarsa a duk lokacin da ya bukace ki. Ki nuna masa ya hakura sai kun yi aure, idan kuwa kika biye masa zaki nadama. 

7:  Nuna bacin ranki akan abunda kika nema baki samu ba. Kada ki nuna damuwarki kan hakan, 

8: Nuna masa yafi kowa mahimmanci a wajenki. Sai dai ki nuna masa a cikin samarin dake neman aurenki babu kamarsa 

9: Yiwa wasu samarin karya ta waya a gabansa. Duk macen dake yin hakan tana rage kimarta wajen namiji. 

10:  Nuna zafin kishinki akansa. Koda zaki yi hakan to kiyi saffa-saffa. 


Wannan Sune abubuwa 10 da mata za su guji yiwa mazajen dake neman aurensu. Da fatan mata kun ilimantu daga wannan abubuwan. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post