Hanyoyin Hana Daukar Ciki Na Maza - Android Pols

Hanyoyin Hana Daukar Ciki Na Maza - Android Pols
Hanyoyin Hana Daukar Ciki Na Maza


Idan mace da namiji zasu yi saduwa a daidai lokacin da yake da wahala macen ta iya daukar ciki, watau jim kadan kafin ta fara al’ada, ko kuma bayan ta kare.


Hanyoyin hana daukar ciki na maza kwaroron roba (condom ko kuma capote): yana kare maza da mata. An yi shi da roba marar kauri, kuma wani kwaroron an shafa masa wani mai mai kara sulbi (santsi), wanda ke kashe kwayoyin halittar da ke cikin maniyyi. Idan za a yi amfani da shi sai an bari azzakarin ya mike ya yi gam tukuna kafin a saka kwaroron robar alokacin da za a sadu.


Amfanin kwararon Roba Wajen Hana Daukar Ciki 

Amfanin kwaroron roba: yawanci yana da saukin samu, ba ya da wata illa a jikin dan adam, yana kare mutum daga cututukan da ake dauka ta hanyar jima’i, da kuma kwayar cutar HIV, sannan kuma yana hana daukar ciki.

Matsalar kwaroron roba: sai an yi amfani da shi yadda ya kamata zai zama da tasiri; yana iya jawo cikas a lokacin yin jima’i. Zuhudu (abstinence) ko kuma kin tarawa a wasu lokuta.

Idan mace da namiji zasu yi saduwa a daidai lokacin da yake da wahala macen ta iya daukar ciki, watau jim kadan kafin ta fara al’ada, ko kuma bayan ta kare.

Amfanin wannan dabarar: ba ta da wata illa a jikin mutum. Domin da wuya a san lokacin yin al’ada ko kuma sakin kwai, musamman ga karamar mace; babu kariya daga cututukan da ake dauka ta hanyar yin jima’i, ko kuma daga kwayar cutar HIV.

Amma ku sani ba kawai amfani da kwararon robar ne ke hana daukar ciki ba, akwai wasu dabarun da ake amfani dasu kamar janye azzakari daga cikin farji kafin namiji yai relizin. 

Namiji zai janye azzakarinsa daga cikin farji kafin ya kawo (ejaculation). Masana sun ce babu wata illa a jiki. Kawai dai wannan dabarar bata da wani tasiri mai karfi saboda ana iya samun kwayoyin halitta a cikin maniyyin da ke fitowa daga azzakari kafin mutum ya kawo; kuma babu kariya daga cututukan da ake dauka ta hanyar tarawa ko kuma kwayar cutar HIV mai haddasa SIDA ko AIDS.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

4 Comments

Previous Post Next Post