Amfanin karo a gaban mace

Amfanin karo a gaban mace
Amfanin karo a gaban mace

Amfanin karo a gaban mace, Karo yana taka muhimmiyar rawa wajen kara lafiya da tsuke gaban mace. 


Shin kunsan amfani da muhimmancin karo a gaban macro? Nasan da yawa daga cikin mata za su yi tunanin cewa karo na da tasiri a gabansu, amma ba abin mamaki bane kuma duk wanda suka taba yin amfani da karo don gyara gabansu nasan sun san hakan. 


Mata da yawa suna yin amfani da abubuwa daban-daban domin samun ni'ima, tsukewa ko ciko da gabansu. Amma da yawa daga cikin abubuwan da mata kan yi amfani dasu suna da illa ga lafiyar su. Hakan yasa na kawo muku karo don yin magani. 


Amfanin karo a gaban mace

Karo yana taka muhimmiyar rawa wajen kara lafiya da tsuke gaban mace. Ga yadda ake yin amfani da karo a gaban mace. 


Ki samu karo ki daka shi ya zama gari, sannan ki dafa shi da ruwa mai kyau ya tafasa, za ki dinga yin tsarki dashi a kullum safiya, rana da kuma dare. 


Ki samu Karo ki zuba ruwa kadan cikin tukunya ki tafasa shi da karon sai ki sauke, zakiga karon ya narke ya yi kauri kamar kakide. Shi wannan za ki dinga lakata kina shafawa a gaban ki ya kwana, da safe ki samu ruwan dumi ki wanke gabanki dashi. 


Ki samu Karo ki dafa shi da ruwa wanda zaki iya yin wanka dashi, idan ya dafu ki zuba a roba ko bahon wanka idan ya huce yadda ba zai kona miki jiki ba sai ki shiga ki zauna na tsawon minti 10 zuwa 15.


Amfanin karo a gaban mace 

Duk macen dake yin amfani da karo ta hanyoyin da muka bayyana a sama zai yi mata wadannan abubuwan;


  1. Zai hade gaban mace ya tsuke ya dawo kamar na sabuwar budurwa. Mace Ko haihuwa nawa tai zai taimaka mata tsukewa
  2. Yana yin maganin fitowar farin ruwa daga gaban mace wanda ake kira da vaginal discharge. 
  3. Yana karawa mace ni'ima, amfanin karo a gaban mace shine yana karawa mace ruwan ni'ima wanda zai sa miji yaji dadin saduwa da ita. 
  4. Yin amfani da karo a gaban mace yana magance dukkan wasu cututtuka na infection musamman na bacteria. 
  5. Sannan yana magance irin kurajen dake fesowa mata a gabansu, da sauran cutuka. 


Wannan shine amfani karo a gaban mace, duk matan dake fama da matsalar rashin ni'ima ko rashin jindadin saduwa, ko kuma matan dake fama da matsalar Cutukan infection dake bayyana a gabansu ku yi amfani da hanyoyin da muka bayyana muku a sama zai taimaka muku wajen magance matsalolin. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post