Alamomin Namijin Da Baya Haihuwa |
Alamomin Namijin Da Baya Haihuwa: kusan dukkan mai aure daya cikin bakwai ana iya samun namijin da baya haihuwa
Da sunan Allah mai Rahama mai jinqai, tsira da aminci su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi MUHAMMAD (SAW).
Yau insha Allah za ku ji bayani akan alamomin namijin da baya haihuwa da kuma abubuwan dake jawo hakan. Da fatan za ku ilimantu da abubuwan da za mu bayani akai.
Male Infertility (rashin Haihuwa Ga Da Namiji) kusan dukkan mai aure daya cikin bakwai ana iya samun namijin da baya haihuwa koda kuwa ya shafe shekara ko fiye da shekara yana saduwa da mace batare da wata kariya ba, misali amfani da kawroron roba ko wata kariya mai kamada wannan. kusan rabin wadannan ma'auratan rashin haihuwa na taka muhimmiyar rawar sabanin zamantakewa a tsakanin su.
Alamomin Namijin Da Baya Haihuwa
Masana lafiya sun bayyana wasu alamomi dake haifar da rashin haihuwa ga namiji, ga jerin alamomi kamar haka;
1) Rashin lafiya namiji, namijin dake fama da wata matsalar rashin lafiya.
2) Cututtukan gado daga gun iyaye na hana namiji haihuwa
3) shan wahala wajen fitar da maniyyi yayin saduwa ko kuma fitar da maniyyi dan kadan yayin saduwa.
4) Rashin jin sha'awar mace ko kuma rashin karfin mazakuta na daga cikin alamomin rashin haihuwa ga namiji.
5) zafin ciwo, kumburi ko kuma alamun cancer ga bangaren marena
6) yawan rashin lafiyar numfashi wadda kananan kwayoyin halitta na microbes ke sawa
7) Rashin jin kamshi ko wari
8) matsalar halittar da namiji inda zakaga namiji da nonuwa masu girma kamar mace
9) Rashin gashin gemu ko kuma gashin jiki wadda alama ce ta chromosomal or hormonal abnormalities
10) Karancin maniyyi yayin saduwa kamar kasa da 15 million per mills ayayin inzali ko kuma kasa da 39 million bayan gama fitar maniyyin duka idan aka auna abunda ka fitar.
Wadannan sune alamomin namijin da baya haihuwa kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayyana. A darasin gaba za mu kawo muku abubuwan dake jawo rashin haihuwa ga namiji.