Alamomin namiji mazinaci - Android Pols

Alamomin namiji mazinaci
Alamomin namiji mazinaci


Masana Sun Bayyana Alamomin namiji mazinaci Da Abinda Ke Jefa Su Neman Mata


Namiji mazinaci shine mai neman matan banza, sai dai ba kowane namiji mai irin wannan dabi'a ake iya gane shi a fili ba domin babu wata alamar dake bayyana a tare dashi dake nuna shi mazinaci ne. Sai dai akwai wasu alamomi na halayya dake nuna namiji mazinaci. 


Alamomin namiji mazinaci

1. Wasu mazan suna zama mazinata ne saboda sun auri ballagaza shashashar mace, wacce bata iya zaman aure ba, wacce bata iya kissa da tarairaya ba. Wacce bata san me rayuwar aure ya kunsa ba. Ita dai kawai gatanan ne.

Babu yin kwalliya ga maigida, babu shafa turaruka masu kamshi da gyara fata, bata shafa mai wanda zai sa fatar ta tayi laushi, bata gyara gashin kanta, bata iya kwanciyar aure ba, bata iya shagwaba mai fisgar hankali ba, bata iya nuna kauna da soyayya ga miji ba. Bata iya zama tayi masa hira domin ya nishadantu ba. 

Bata iya magana ba, bata iya kallo ba. Ita dai gata nan ne kawai. Toh kun ga mijinta baya samun abin da ya kamata ya samu a wurinta, mai yayi saura? Sai yaje ya fara biye-biyen mata mazinata, idan baida tsoron Allah. Kin ga kina daya daga cikin mutanen da suka bashi gudunmuwa wurin jefashi cikin wannan musiba ta yin zina. 

2. Wani kuma namijin yana zama mazinaci ne saboda mabukaci ne da yawa, ita kuma matar bata iya jure masa, har ya kai ga duk lokacin da zai nemeta sai anyi rigima, toh a nan idan mijinki ya bukaci kara aure, kada ki hana shi, idan kuma kika yi masifa kika tayar masa da hankali toh zai kuwa fada neman mata, kina zaune zai kawo miki tsarabar HIV/AIDS har cikin dakinki. Don haka ki kyale shi yayi aurensa don wani baya iya hakuri da mace daya.

3. Wata kuma ta iya kwalliya da kissa, da tarairaiya, da abinci, da tsafta, ta iya kwanciya da komai, amma mijinta kuma mazinaci ne yana neman mata, to irin wadannan sai ace jarabawace, domin basa daga alamomin namiji mazinaci, domin irin wainnan mazan ko mata 100 za'a tara musu to ba zai hana idan sun ga wata su nema ba. Domin su basu dauki aure a bakin komai ba. Ki dage sosai da rokon Allah, sannan kada ki fasa abin da kike masa na kyautatawa, ki cigaba, da izinin Allah zai dai na wata rana.

Sannan ki rinka kokarin nuna masa illan yin hakan, misali: Kice wane Idan ni kadai bana isan kane to ni babu damuwa ka karo wata, saboda ina ji maka tsoron cuta, domin bana son ka zama namiji mazinaci, kuma ina jiye maka tsoron kada abin da kayi ma 'ya'yan wasu ayi ma naka.

Magana zaki yi masa cikin nutsuwa da ladabi, a kuma lokacin da kika ga ya cancanta. Ki rinka yi masa magana cikin nutsuwa da sanyin murya. Kada ki nuna masa kina fushi, kada ki nuna bacin rai. In ma zaki yi kada ya wuce kina magana kina zubar masa da kwallah na nuna bakin ciki da damuwa. Idan kina masa haka, kuma kina ribanya abubuwan da kike masa na kyautatawa. Da izinin Allah zai dai na.

Sannan Addu'a, shi zaki dage da yi don Kada mijinki ya zama mazinaci, babu dare babu rana, In Allah yarda za a wayi gari ya dai na ya dawo gareki.

Maza kuji tsoron Allah ku dai na shiga hurumin da ba naku ba, zina haramunce har ranar alkiyama, ka tausayawa kanka da matar ka, sannan ka tausayawa zuri'arka, kada su taso a neme su, a lalata maka rayuwarsu. Na tabbatar ba zaka so ba.

Allah ya kubutar da maza masu fama da wannan matsala ta zina. Wannan Sune daga cikin alamomin namiji mazinaci, wanda galibi mata sune suke jefa mazajensu cikin neman matan banza suna zina dasu. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post