Alamomin Jinin Haila Da Hanyoyin Da Mace Za Ta Kula Da Kanta

Alamomin Jinin Haila Da Hanyoyin Da Mace Za Ta Kula Da Kanta
Alamomin Jinin Haila 


Zuwan Jinin Haila Da Yadda Zaki Kula Da Kanki Yayin Zuwansa 


Haila, al'ada, jini, mensis ko ace period duk sunayen abu guda ne. Haila wata abace da Allah ya tsara ga dukkan 'ya'yan Adam musamman mata wadanda suka cimma wasu shekaru na rayuwa na fara aikin wasu sinadaren halittun jima'i dake jikinsu da ake kira (estrogen And progesterone) a dukkan lokaci lokaci.


Haila itace babbar alama dake nuna mace bata da juna biyu, sannan itace babbar alama dake nuna jikin mace shirye yake da ya dauki juna biyu idan har da zata samu yin Jima'i tsakaninta da namiji.


Su sinadaran Progesterone da Estrogen dama jariri na samun su tun aciki yayin da halittar mutum takai sati 12, amma basa fara aiki sai mace takai shekarun balaga.


Balaga kan bambanta wasu tun ashekara 9 suna iya fara haila don haka balagarsu kenan, wasu a shekara 11, amma da yawa sunfi farawa daga shekara 13- ko -14, sai dai masu raunin wadannan sinadaren wasu sukan kai har shekara 17 basu fara ba koma 19. Irinsu ne saikaga ga girma da tsayi ajiki amma idan ka kallesu babu bambanci da jikin yara wato ba fashewar kugu babu alamun fitowar nonuwa.


Haila a mafı yawa takan zo duk bayan kwana 28 kuma Sannan yawanci kwanakin basa wuce 5, sai dai dake Allah yai mana halittu daban-daban wasu sukan sami tazarar kwana 30 zuwa 37 sannan su kuma yin wata hailar, kuma haka jikinsu yake ba matsala bace. Wasu kuma duk bayan kwana 21.


Wasu sukan ga haila ta dauke musu har wata 1, 2 ko 3, toh idan mai aure ce idan haka ta faru yawanci juna biyu shine abunda muke tsammani, idan ma baki da aure kuma baki da kamun kai to kema haka muna tsammanin juna biyu ne.


Toh amma idan duk anyi gwaji babu juna babu ko daya to sannan ake fara tunanin wasu abubuwan dakan jawo daukewarta kamar haka:


  • Idan mace tai fama da rashin Ify a tsakanin,
  • Ko idan mace ta bada gudunmawar jini,
  • Ko macen dake shan kwayoyin bada tazara,
  • Ko mai shan maganin larurar hawan jini,
  • Ko Shan maganin ciwon suga,
  • Ko sakamakon hatsari,
  • Karancin jini
  • Ko samun kai a halin kunci da damuwa (depressed),
  • Ko samun kai a halin tsoro da fargaba (Anxiety)
  • Ko idan wata mutuwa me zafi ta faru cikin dangi


Duk wadannan ka iya sa mace taga hailarta batazo ba matukar ba juna biyu gareta ba.


Shin yana yiwuwa mace tai haila alhalin tana da juna biyu?

Magana ta gaskiya kuma wacce na sani kuma nake akanta shine bazai taba yiwuwa ba ace mace nada juna biyu kuma tana haila. Abunda ke janyo wannan jinin yawanci daga bakin mahaifa ne sakamakon Kila yawan saduwa da ita da ake hakan kan sa cervix din yai rauni, wannan tasa bamason ake saduwa da mace mai karamin ciki akai akai har zuwa watanni 4 ko kuma a dalilin yagewar wani sashi na mahaifa ko hujewa kila sakamakon ko ta hau mashin ko mota tai doguwar tafiya. 


Ko alamar tsiron cikin mahaifa, ko kansar bakin mahaifansu, Ko kuma Kila d'an dake cikinta ne ya gicciye ba daidai ba, ko kuma sakamakon wajen awo ansa hannu an gyara yaro ko wani abu wanda Kila daga nan jinin yaci gaba da fita. Amma gaskiya bazai yiwu ana goyon ciki ana haila ba saboda kwata kwata ma ayyukan hormones din sunyi hannun riga da hakan, don haka zataje aduba ta agane dalilin jinin abata magani.


Sannan ba'a cewa haila ta shiga matsala ko kuwa sa kai a damuwa har sai mace taga tai wata 6 batare da ganin hailar ba sannan zatai tunanin abunyi wanda shine muke Kira (amenorrhea) wato daukewar haila.


Amma dan tana samun tazarar wata 2, 3 zuwa 4 ko 5 wannan shi muke Kira abnormal wato (oligorrhea) tana al'ada amma ba akai akai ba, Bakuma matsala bace. Kila 1 daga cikin abubuwan dana lissafa a sama ne ke faruwa. 


Macen da bata al'ada akai akai wannan kesa wasu aga suna fitar da gashi a fuskarsu, wasu kuma gashin su ya rika zubewa, wasu yawan ciwon kai, wasu kuma su rika ganin ruwa in sun matsa Kan nonon su koda kuwa yan matane basu da aure.


Shin Ko Za'a Iya Samun Ciki Kwana 2 Kafin Al'ada Sannan Yaya Alamominsa Yake? 

Ai indai anga haila toh babu zancen ana da ciki. Sannan ba koyaushe ciki ke shiga ba. Yawanci macen dake kwana 28 kafın haila ta zagayo kwanakin daukar cikinta kan kasance kwanaki 11, 12, 13, 14 koma 15 bayan daukewar waccan hailar ta baya.


Shawarwari A Kan Yadda Zaku Kula Da Kanku 

Sau da dama a lokacin jinin al'ada mata kan shiga halin tasku, inda wadansu kan kauracewa shiga cikin mutane, wanda kuma ke takurawa rayuwarsu har su samu kansu kamar an sanya musu takunkumi. Tunda a zahiri musamman haila a lokacin zafı har canjin smelling ajikin mace na fuskanta kuma ko ta sa turare wata bata yadda da kanta ta saki jiki.


Hakan ne ya sanya zan yi muku bayanin yadda zaki lura da kanki a lokacin jinin al'ada har ki samu sakewa da kuma walawa.


1]. Kwantar Da Hankali, Ki nutsu ba'a so ki tayar da hankalinki don kin fara ganin jinin al'adarki, hakan zai sanya mata yan uwanki ko mahaifiya har su fahimci halin da kike ciki. Don haka ki kwantar da hankalinki kamar babu wani abu da yake faruwa dake. Ki dauka kamar kowa kike babu kuma wanda zai gane komi


2]. Ki kasance dauke da 'Pad' ko 'Tampon', a kowane lokaci don gujewa jin kunya tunda wasu jinin na fita da yawa.


3]. Canja 'PAD', Ya kamata ki rika canza 'pad' ko 'tampon' duk bayan awa 4 zuwa 8, idan kuma jinin yana zuba sosai sai ki rika canzawa lokaci zuwa lokaci koda awa bi biyune, domin lokacin da jinin ya gama jiqa 'pad' ko 'tampon' din. Barin 'pad' ko 'tampon' ya dade zai sanya samuwar kwayoyin cutar bakteriya musamman wacce muke kira STAPH AUREUS, domin jini ba karamin daula ke zame musu ba wajen rayuwa wanda hakan kuma zai haifar miki da matsala ta kwayoyin cuta acikin jini da guiwoyi wato SEPSIS. Wanda idan ba a dau mataki ba mutuwa ma na iya faruwa musamman mace me karancin tsafta.


Shyasa nake kira ga yayye maza kuke taimakon kannenku mata da kudin pads duk wata kudena barinsu da roke roken samari, wasu ma saboda babu saide su nemi soson katifa ko dan kwali su yu kunzugu kunga bai dace ba, don haka ku taimaka musu.


4]. Lura Da Κai, Daga lokacin da akace an fara al'ada, tsabtace kai na da matukar wahalar gaske. Musamman lokacin zafı, daga an yi gumi sai a fara wari mai tayar da zuciya, har mutane su rika kyamar wacce ke jinin al'ada.


Don gujewa hakan sai ki rika wanka lokaci zuwa lokaci, hade da shafa turare mai tafıyar da wari (deodorant), sannan ya kamata ki goge bakinki sau biyu ko uku a rana domin hakan zai magance miki warin bakin dake fitowa daga baki lokacin jinin al'ada. Bayan haka ki rika cin cingam mai kamshi, ko tsotsar minti ko cin cakulat.


5]. Lura Da Kuraje, Wadansu matan idan za su fara ko kuma sun fara jinin al'ada kurajen kan fito musu, to idan kina daya daga cikin wadannan matan, idan kurajen sun fito miki, kada ki fasa su, ko kuma ki rika taba su. Abin da za ki yi shine, ki rika wanke fuskarki sau biyu ko uku a rana. Ko kuma ki wanke fuskarki daga zarar kin fara gumi idan lokacin zafi ne.


6]. Lokacin Al'ada,  Yawancin kwanakin al'ada basa wuce 3 zuwa 7. Duk lokacin da jinin al'ada yazo miki to zaki samu na gaba yazo a wani lokaci daban, duk da cewa wadansu kan samu tazarar kwana 28 ko 35 kafın wani jinin yazomusu. Don haka ina baki shawara ki ajiye karamar kalanda a dakinki ko ki saita kalandar cikin wayarki. Hakan zai ba ki damar fahimtar lokutan al'adarki, kuma zai ba ki damar lura da kanki ba tare da wani ya gane ba.


7. Jin Zafi, Baban abunda ke jawo ciwon mara a yan mata rashin saduwa da basa samu, toh amma in na hade batun gaba daya dana masu auren Lokutan al'ada kanzo da ciwon ciki, ciwon kai ko murdawar mara, hakan na faruwa ne sakamakon matso jinin da mahaifa keyi wato uterus contraction, hakan kan sanya takura.


Hanyar da zaki rage hakan shine ki rika motsa jikinki, misali ki rika kai ziyara ga 'yan uwa da abokan arziki, shan tea me citta sosai. Sannan magunguna irinsu paracetamol, diclofenac ko mist pot Cit na ruwa na taimakawa wajen tafı da zogin amma dai a tabbatar ana amfani dasu bisa ka'ida. Amma idan ciwon cikin, ko kai, ko kuma murdawar marar ta tsananta sai ki nemi likita.


Sannan a karshe ga masu fuskantar heavy bleeding wato jinin ya rika fita da yawa gaskya inde ko yaushe haka kike to ki daure kiga likita mafi yawa karin cikin mahaifa Kan jawo haka wato fibroids. Allah sa mu Gama Ify, ya kara muna Ify amin


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post