Abubuwa 4 Dake Janhankalin Namiji Yaso Matarsa

Abubuwa 4 Dake Janhankalin Namiji Yaso Matarsa
Abubuwa 4 Dake Janhankalin Namiji Yaso Matarsa 


Idan Mace Na So Ta Mallake Mijinta Akwai Abubuwa 4 Wanda Idan Tana Yimasa Zai Kara Sonta Da Kaunata


Akwai wasu muhimman abubuwa 4 wanda har idan mace na yi wa mijinta su zata kara shiga ransa har yaji babu wata mace kamar ita. Sai dai samun mace mai yin irin wannan abubuwan yana da wuya. Amma Indai kina so ki Mallake mijinki cikin sauki kiyi kokari ki yi masa wadannan abubuwan ki sha mamaki. 

1) Tsafta: kowanna namiji yana matukar son tsafta, kuma kowane namiji ya tsani kazanta koda shi kazamine dazarar mace ta zama mai tsabta hakan zai zama abun yabo agun mijinta da karamata kima agunsa. Tsafta na sa makota ma da yan uwanki mata suso abun da kikataba, hakanan kazanta nasa kowa yatsaneki ballantana mijinki ma.

2) Kwalliya: kwalliya na maida mace babba kamar budurwa hakama rashin kwalliya na mayar da mace kamar dodanniya, ita mace batada wani kyau azahirinta idan batayi kwalliya ba, yawanci rashin kwalliya nasa wasu mazan su bar matansu kyawawa a gida suje neman munana a kwararo saboda sun iya kwalliya. Don haka yar uwa ki koyi kwalliya a gidan mijinki bawai sai zaki gidan biki ba. Don haka ki tsaya kuma ki koyi yadda akeyin kwalliya mai kyau ba wacce zata maidake kamar dodanniyaba alhalin komai miji yasayo yabaki.

3) Girki: kowannan namiji yana alfahari da girkin matarsa yakan zuzutata akan ta iya girki koda bahakabane, dazarar kin iya girki zakina gani mijinki na gaiyato abokansa kala kala hakan kuma na burgeshi, na fasa masa kai, amma dazarar baki iya girki ba shima bazai naci ba sosai ballantana ma yagaiyato wasu abokansa. Dan haka lallai ki zama me iya girki kala kala dan kula da mijinki.

4) Kula da hakkin kwanciya: itama wannan na daga cikin abu mafi girma dake sa mace mallake miji wato bashi hakkinsa na kwanciya a duk lokacin da ya bukata, hakanan kuma hana mai gida hakkinsa na kwanciya nasa miji ya tsaneki yai miki kishiya ko ma  ya koreki bayan fushin Allah.


Wannan sune abubuwa 4 dake jan hankalin namiji yaso matarsa har yaji babu kamarta, shin kina iya yin wadannan abubuwan ko bakya yi? Idan har baki yi daga yau ki fara za kiga kulawa sosai daga wajen mijinki. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post