Zafafan Sakon So Na Barka Da Safiya Ga Masoya - Android Pols

Aisha Aliyu Tsamiya: Zafafan Sakon So Na Barka Da Safiya Ga Masoya
Zafafan Sakon So Na Barka Da Safiya Ga Masoya 


Sakon So: Zanso ace kamar yanda nake jin karsashin kaunarki cikin zuciyata tun dare njiya, zan so ace ke ma hakane


Kai kadai zan turowa sassanyan sakon sanyaya ruhi da zuciyata, tun da sassafe, amma kafin in turo sakon sai na jera jadawalin jaddada tambayar kintashi lfy kyakykywar sauniyata?


Zanso ace kamar yanda nake jin karsashin kaunarki cikin zuciyata tun dare njiya, zan so ace ke ma hakane, domin hakan ya samo asaline tun rabuwarmu ta jiya da dare domin silar tozali da walwalar kyakykywar fuskarki dauke da murmushinki mai baiwa zuciyata  daddadan farin cikin dake sanya ruhina ya sa na gamsu cewa da rai nake sonki bada zuciyata,


kwana nake da tinanin kyakykywar suffarki ne yasa tashina ke da wuya na turomiki sakon barka da safiyar yau saruniyata. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post