Yadda Za Ka Mallaki AL-Jani Ya Dinga Yi Maka Aiki

Yadda Za Ka Mallaki AL-Jani Ya Dinga Yi Maka Aiki
Yadda Za Ka Mallaki AL-Jani Ya Dinga Yi Maka Aiki 


Yadda Za Ka Mallaki AL-Jani Ya Dinga Yi Maka Aiki 


A wani binciken da Shafin Sunnah Medicine ya gabatar, ya gano cewa, hanya daya cikin hudu mutum zai bi domin ya mallaki Aljani, ya dinga yi ma sa aiki. 

بسم الله، والصلاة والسلام على رسول الله، وبعد:-


1)-Hanya ta farko ta mallakar Aljani ko Aljanu da yawa, ita ce mutum ya sadaukar da ruhinsa da gangar jikinsa ga Aljani domin ya dinga biya masa bukata. 


Ita wannan hanya ta mallakar Aljani, ta fi kowacce hanya tsantsar kafurci da shirka. Ta yadda mutum zai amince cewa ya zama bawan Aljani kuma ya barranata kansa da Allah Mahaliccin halitta baki daya. Wannan hanya tana da hanyoyi daban-daban kusan guda bakwai, wadanda na taɓa kawo bayanin hanyoyin dalla-dalla kusan shekaru uku da suka wuce. A takaice dai wasu daga cikinta su ne akwai:-

i) Dariqatuz zab'hi طريقة الذبح

Wato hanyar yanka, ta yadda mutum zai dinga yankawa Aljanu wata dabba suna shan jininta. Kowa ya san duk wanda yayi wa wanin Allah yanka to ya zama mushriki


ii) - Akwai Dariqatul Tankiys طريقة التنكيس

Wato hanyar da mutum zai dinga wulakanta Alqur'ani ko kuma canja Alqur'ani daga ainihinsa. Misali a hada ayoyin Alqur'ani da sunayen wasu Shaidanu a dinga karantawa a tare ko a rubuta wata aya gaba-abaya ko kuma a rubuta Alqur'ani da jinin haila ko a saka shi a cikin kazanta. Ya kuma hada da buda wasu haruffa na Alqur'ani a saka wasu sunaye aciki. Cikakken bayani dai akan wannan hanya yana nan acikin littafin 'Assarimul battar'. 


iii) Sannan akwai hanyar da mutum zai dinga yin wata ibada ta musamman saboda Aljanu. Kamar ya ajjiye wani gunki, ya dinga yi masa sujjada. Wani za su saka masa sharadin ya dinga zama da janaba ko ya dena sallah ko karatun Alqur'ani. Daga cikin masu bin irin wannan hanya akwai wanda ko sallama ba ya amsawa, wani ma idan zai baiwa mace magani zai gaya mata cewa ta bari sai lokacun da take haila sannan ta zo, ko namiji ace lokacin da yake da najasa, sannan za a saurare shi. 


iv) Daga cikin kazantar wannan hanya, akwai wanda Aljanu suke luwadi da shi da sauran ayyukan kazanta. 


Da dai sauran hanyoyi da dama. Mai son karanta cikakken bayani akan ragowar hanyoyin sai ya duba rutun da nayi akan 'Siffofin Bokaye ko Yadda ake gane boka'. 


To Boka ma'abocin wannan hanya ta farko, ma'ana 'Hanyar sadaukar da ruhi da gangar jiki ga Aljanu', ya fi saurin tara masifaffun Aljanu masu yawan gaske kuma 'yan bala'i. Yawancinsu ko kuma dukkansu arna ne marasa imani, wadanda ake saka su ayyukan kisa da sauran muggan laifuka. 


Sai dai Boka mai bin wannan hanya ya fi sauran bokaye shiga cikin hadari da sharrin Aljan. Domin a duk lokacin da ya saɓawa Aljanunsa to za su yanke masa hukuncin kisa ne ko su haukata shi, ko su kashe masa iyalansa ko su koma jikinsu. Haka nan daga cikin sharadan da suke sanyawa mai aiki da su shi ne, ba su yarda ya tuba ko ya daina aikin ba, haka nan ko ya mutu sai sun koma jikin 'ya'yansa sannan ba za su taɓa tashi daga gida ko wajen da yake aikin da su ba, komai tsawon shekaru. 


Domin kuwa sai ya amince ya gina musu mahalli na dindindin a wajen. Idan tafiya tay tafiya ma za su ce ba su yarda ya dinga karɓar kudi ba ko kuma duk kudin da ya samu sai dai ya kona ko ya rabawa mutane kuma dole ya bi su, don gudun fadawa masifarsu. Shi yasa za ka ga Boka a ƙungurmin daji ko acikin gida kwararraɓaɓɓe, 'ya'yansa da matayensa da shi kansa duk a cikin wahala da talauci, ga shi manyan attajirai suna zuwa suna kawo masa kudi, sai ka rasa yadda yakeyi da su. Kuma ko ya mutu 'ya'yansa ba abinda za su gada sai tarkacen kayan bokanci da bakaken Aljanu, domin duk Aljanunsa sun sa ya lalatar da abinda ya samu. 

Da dai matsaloli da yawan gaske. Duk bokan da ke bin wannan hanya karshensa mutuwar wulakanci, wasu malamanma sun ce ba ya cikawa da imani, ga shi duniyarma ba tayi masa dadi ba. Allah Ya tsare mu. 


2)- Hanya ta biyu ta Mallakar Aljanu ita ce, a kafa kamfani tsakanin Aljani da mutum, duk ribar da aka samu sai a dinga rabawa, kowa ya dauki nasa. 


Wannan hanyar itama akwai shirka acikinta da kuma tsabagen karya da yaudara ta fuskar Aljanun, kuma itama tana da hadari, saidai ba ta kai hanya ta farko ba amma dai dukkansu ɓata ne. Wato Aljanin zai dinga yiwa bokan aiki, in ya so duk kudin da bokan ya samu sai a raba, ya dauki nasa, ragowar kuma ya baiwa Aljanin. Wasu Aljanun suna karɓar kudi cash, wasu kuma su ce ya siyo musu dabba su sha jininta, wasu su ce ya je gidan tururuwa ko cikin shuri, ya zuba kudin, wasu kuma su ce ya siyo musu bakaken kaya ko jajaye kodai wata kala da suke bukata. Akwai kuma wadanda za su cewa bokan ya tafi waje kaza, daidai lokaci kaza, zai ga wani mutum mai siffa kaza, sai ya ba shi kudin. 


Bokan da ke bin wannan hanya, ya fi sauran bokaye saurin tara kudi na fitar hankali da samun daukaka da farin jini cikin kankanin lokaci sannan ya fi sauran bokaye yin abubuwan mamaki, kamar ya dinga buga kudin jabu ko baiwa ɓarayi sa'a da sauran abubuwan 'badali بدل' da tahriqul adat, kamar ka ga mutum ya saki carbinsa kuma carbin ya tsaya a sama, bai fado ba. Nan da nan za ka ga mutum yana samun kudi yana gine-gine, yana hawa motoci. 


Sai dai kash, mabiya irin wannan hanya ba sa dadewa suna yi, da zarar mutane sun fara ganosu cewa macuta ne, sai samun kudinsu ya fara raguwa, daga nan sai Aljanun duk su gudu, su barsu, tunda kasuwancin ya fara samun matsala. Sai kuma Mallam ya koma damfarar mutane da cin bashi, karshe ya fada talauci, duk ya siyar da abubuwan da ya tara, ya koma matalauci, har jama'a su dinga tausaya masa. Ma su bin irin wannan hanya yawanci ba sa karewa da mutane lafiya, domin akasarinsu bayan Aljanun sun barsu sai kuma asirinsu ya fara tonuwa, ka ga mutane suna kai su kotu da sunan sun ci kudinsu, sai ka ga sai dai mutum yai hijira ko ya kare a kurkuku. Mutane da yawa shaida ne akan yadda ta ke karewa da shahararrun bokaye. 


Aljanu masu wannan halayya ta kashe-mu-raba da bokaye, ba sa aiki da kowa sai matashi, mai ji da kuruciya, idan ya fara tsufa ko kuma samun kudinsa ya ragu sai su hada shi rigima da mutane, su gudu, su bar shi. Da dai matsaloli da yawa gaskiya. Allah Ka raba mu da sharrin duniya. 


3)- Hanyar Mallakar Aljani ta uku kuma ita ce - Mallakar Aljani ta karfin tsiya, ta hanyar yin amfani da Sarakunan Aljanu ko kuma amfani da hanyoyin tsafi, ta yadda za a tsafe Aljanin, ya dinga yin aiki ala dole. 


Hanyoyi ne guda biyu. 

Ta farko wata hanya ce ta tsantsanta bauta ga wanin Allah, ta yadda mutum zai nemi taimakon Sarakunan Aljanu da neman kusanci a garesu ta hanyar allantar da su ko neman taimakonsu. Wato mutum zai kaskantar da kansa a garesu ta hanyar yin wuridin sunayensu ko amfani da wasu nau'ukan turaruka da suke bukata ko ziyartar mazaunansu da kuma neman su tallafa masa da hadiman Aljanu. Sai dai Malamai sun ce, wannan hanyar itama, tsantsar kafurcin da ke cikinta kamar hanya ta farko ce, domin sai mutum ya zama cikakken bawan shaidan kuma barranta kansa da Allah Madaukakin Sarki sannan suke amincewa da shi.


To sai Sarkin Aljanu ya zaɓo wawaye acikin bayinsa ya mallakawa wannan mutumi, shi kenan sai ya cigaba da tasrifi da su. Duk Aljanin da ya saɓa masa kuma sai ya kai kararsa wajen Sarkin Aljanu, shi kuma ya hukunta shi.


 Bangare na biyu acikin wannan hanya ta Mallakar Aljanu kuma ita ce mutum ya mallaki Aljani ta hanyar tsafi da sihiri. Misali, akwai mutanen da su ka iya danawa Aljani tarko kamar yadda ake danawa ɓera tarko kuma su kama shi. Wasu sukan dana tarkon a makabarta wasu su dana a tsakiyar daji, lokacin da hasken farin wata ya kai daren sha hudu. Akwai dai hanyoyi da dama da ake bi domin a kama Aljani a hannu, kuma wannan ba wani sabon abu bane, sananne ne a wajen kowa, domin har turawa ma suna yi. To masu amfani da wannan hanya, su kan kama Aljanu da yawa, su ajjiyesu, ta yadda za su dinga saka su ayyuka masu wahala sannan Alajnun suna yi ala tilas. 


Bokan da ke amfani da irin wannan hanya to in ya turawa mutum Aljani gaskiya ba karamar wahala ake sha da shi ba. Irinsu za ka ji in an zo rukiyyah sai Aljanin ya ce shi ba zai fita ba, domin idan ya fita bokan ya ce sai ya kashe shi ko kuma zai kashe masa iyayensa. Wani Aljanin ma shi kansa bai san ta yadda akai bokan ya saka shi ajikin mutum ba kuma bai san ta yadda zai fita ba. Za ka samu suna matukar tsoron bokan domin gani suke kamar shi ne allansu. Aljanu da yawa da suke jikin mutane ba a son ransu suke zaune ba kuma inda sun san wata hanya da su bi su fita to da sun fita, musamman wadanda aka turosu ta wannan hanya. 


Irin wannan bokan Aljanu suna matukar tsoronsa tare da yi masa biyayya kuma yana hukunta su ne ta hanyar dauri ko ya sa manyansu su azabtar da su, wani ma ya kan yankewa Aljani hukuncin kisa. 


To amma fa mai amfani da wannan hanya, bayan kasancewarsa Boka, Mushriki kuma arne, to yana cikin hadarin gaske. Bokan da ke bin wannan hanya kusan ya fi dukkan bokayen duniya fuskantar barazana daga sharrin Aljanu, kuma ko da ransa ko bayan mutuwarsa sai Aljanu sun dau fansa akansa ko akan 'ya'yansa. Kasancewar yana tilasta musu su yi masa biyayya, sai hakan ta sa ya zama babu soyayya ko kauna ko amana kwata-kwata a tsakaninsu, suna matukar jin haushinsa da kuma fatan su samu wata dama da za su nuna masa shayi-ruwa ne. 


Don haka a duk lokacin da yai sake ko Allah Ya jarrabe shi, Aljanun su ka samu wata dama akansa, to kuwa za su kashe shi a take, ko su haukata shi ko su kama iyalansa ko su hada masa gobara. Gaskiya irin wannan bokan shi kansa ba shi da kwanciyar hankali, domin zai ta fama da mafarkai masu abun tsoro da yawan firgita. Wani ma za ka ga yana ba da magungunan Aljanun amma shi kansa a firgice ya ke. Da za a yi masa ruqiyyah Allah ne kadai ya san Aljanun da za a cire masa. Gaskiya dai wannan hanyar itama ɓata ce da kuma shirka. Allah Ya kiyaye mu. 


4)- Hanyar mallakar Aljanu ta hudu kuma ta karshe, ita ce shi Aljanin da kansa ya bijirowa mutum, ya ce yana so ya dinga taimaka masa ko su dinga yin aiki tare. 


Wannan ta kan faru ta hanyoyi daban-daban. Misali, idan mutum ba shi da lafiya yana matsalar Aljanu, sai ka ji Aljanun sun ce zai samu lafiya amma suna so ya dinga ba da magani, ma'ana su dinga taimaka masa, yana baiwa al'uma magunguna. Wani lokacin kuma idan kana ruqiyyah ko kana bada magungunan Aljanu, sai Aljanun su dinga zuwar ma ka, suna cewa suna so su taya ka ko su taimakeka akan aikinka. Na yi cikakken bayani akan 'Aljanu masu shiga jikin masu rukiyyah da masu nazari akan rayuwar Aljanu.


Wani mutumin kuma yana tafe a hanya ma zai gamu da su, su bayyana masa cewa suna so su taimaka masa, wani kuma a mafarki suke zuwar masa da bayanin. Galibin irin wadannan Aljanu su kan nunawa mutum cewa su 'Rauhanay' ne ko musulman Aljanu kuma sukan nunawa mutum cewa ya dinga yawan ibada da sadaka da sauran ayyukan addini. Karanta cikakken bayani akan 'Su waye Rauhanay, acikin wannan shudin rubutun. 


Kamar yadda ka ga bayani, inda ka karanta abinda ke cikin wannan shudin rubutun, to yawancin wadannan Aljanu karya sukeyi, munafukai ne, wasu ma arna ne ba musulami bane, domin sai bayan ka amin ce da su sannan za ka gano hakan. 


Irin wadannan nau'in Aljanu, sun fi shiga jikin mata, da kuma jahilan mutane. Za ka ji wata matar ta ce ta ga Annabi صلى الله عليه وسلم acikin dakinta, har ya ce ta dinga baiwa mutane magani, wata ta ce Nana Fadima ta bayyana a bangon dakinta, har da wadanda wasu Shehunai suke zuwa musu. Na taɓa dora muku videon wata mata, wacce ta ce Manzon Allah صلى الله عليه وسلم

yana zuwa wajenta, har yana hanata sallah da cin abinci kuma ya ce ta fito ta bayyanawa mutane cewa ita 'yarsa ce, har yanzu bidion yana nan a shafina na 'youtube', shiga wannan shudin rubutun ka kalleta kuma ka ji da bakinta


Haka nan na taɓa dora muku hirarmu da wani Aljani, wanda yake zuwarwa wata yarinya, yana cewa shi ne Annabi Muhammad صلى الله عليه وسلم، har ya bata sadakar gashi, ya ce a dinga jikawa marasa lafiya. Shiga wannan shudin rubutun ka saurari hirarmu da Aljanin, ka ji yadda yake bayani da bakinsa. 


Sannan wadannan Aljanu, idan suka ga mutum mai kokarin ibada amma kuma ba shi da ilimi, sai su dinga zuwar masa da siga daban-daban kuma suna yi masa hidima iri-iri, kamar yi masa kudi da abinci da wasu abubuwa da yake bukata, mutumin da ya gamu da irin wadannan Aljanu, yawanci sukan hana shi sallah, su kan sa ya dinga dauka cewa ya zama Allah (wal iyazu billah) ko ya zama Annabi. Su ma ma'abota wannan hanya cikakkun arna suke zama kuma suna samun mataslar kwakwalwa, domin a mafi yawa suna zuwa da abubuwan da mutane suke karyatawa, su kuma su dage cewa gaskiya ne. 


Sai dai ana iya ceto rayuwarsu ta hanyar yi musu rukiyah acire musu Aljanun, in hankalin mutum ya dawo jikinsa shikenan, sai kaga ya dena wadannan abubuwa, kamar yadda na yiwa mutane da yawa, mata da maza masu irin wanna aƙida rukiyyah kuma an cire musu Aljanun, sun gano makaryata ne, walhamdu lillah. 


To Allah Ya datar mu.

Na yi wannan bayani ne musamman saboda wadanda suke marmarin su mallaki Aljani ya dinga yi musu aiki ko kuma suke sha'awar masu aiki da Aljanu. To ga fili nan, ga mai doki. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post