Yadda Ake Gane Budurwa A Daren Farko Na Aure

Yadda Ake Gane Budurwa A Daren Farko Na Aure
Yadda Ake Gane Budurwa A Daren Farko Na Aure Daren Farko: Idan har budurwa ka aura tun a daren farko zaka tabbatar da budurcinta 


Zuwa ga amarya da ango, abu na farko da zaku saka a ranku shine, ita fa kwanciyar aure musamman a daren farko ba kamar yacce kuke kallo a fina-finan turawa na tsiraici bane. Shi wancan film ne akwai director da producer, wannan kuwa kune yan wasa kuma kune masu shiryawa da bayar da umarni. 


Yadda Ake Gane Budurwa A Daren Farko 

Idan har budurwa ka aura tun a daren farko zaka tabbatar, kada ka yi tunanin za ta iya sarrafa ka yadda kake kallo ana yi, koda kuwa tana da ilimi da wayewa, haka kema kada ki yi tsammanin zai iya sarrafa ki 100% musamman idan saurayi kika aura wanda be taba saduwa da mace ba.

Ita kwanciyar aure a hankali za ku dinga fahimtar junanku ba wai a daren farko ba, a hankali za ku yi har ku gane wajen da kowannenku ya fi so a taba masa ko a fi ba shi kulawa, da yanayin salon kwanciyar da dayanku ya fi so, da dukkan abubuwan da suka shafi jindadin jima'i.

Sannan babban abinda ma'aurata suka rasa shine communication, abune me kyau miji da mata su dinga samun wani lokaci da zasu dinga tattaunawa a kan kwanciyar aure bayan daren farko, a lokacin budurwa ko matarka za ta fada maka wajen da tafi son jin dadi idan aka yi mata wasa dashi, da salon da ya fi burge ki, da duk abinda zai taimaka miki ki samu gamsuwa, shima kuma ya fadi miki nashi bangaren, da haka sai ku ga zaku iya gamsar da junanku ba tare da kun zo social media neman shawara ba.

Sannan kowannenku ya mayar da hankali wajen gamsar da partner nashi, kada ku kasance masu son kai, koda yake shi daren farko ma'aurata ba su fiya mayar da hankali wajen Jima'i ba. sai ya kasance ana cutar da wani sashe. Allah Ya bada zaman lafiya.

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post