Maza Gareku: Illolin Yin Chatting A Social Media Da Matar Aure

Maza Gareku: Illolin Yin Chatting A Social Media Da Matar Aure
Maza Gareku: Illolin Yin Chatting A Social Media Da Matar Aure 


Illolin Dake Tattare Da Yin Chatting A Social Media Da Matan Aure 


Ina maza masu yin chat a social media don neman mata/ko matan dake neman maza da niyyar yin Zina dasu? To albishirinku, Kafin kuce goro ga wata 'yar gajeruwar sanarwa daga bakin da baya ƙarya.


Manzon Allah (SAW) yace: Wanda ya yi Zina da wata mata musulma ko bayahudiya, ko kirista, ko bamagujiya, ko baiwa, Sannan bai tuba ba, kuma ya ci gaba da hakan, To Allah zai buɗe masa ƙofofi ɗari uku (300) A cikin kabarinsa da macizai da kunamun wuta za su riƙa fitowa suna saransa da cizonsa yana ƙonewa har a tashi ƙiyama. 


Idan kuwa aka taso shi daga kabari to mutane za su cutu daga warinsa ,Sai a gane shi da wannan a kuma gane me yake yi a duniya, har sai ayi umarni da shi zuwa wuta.


Manzon Allah (SAW) Yace ''Duk mutumin da yayi Zina da matar Aure Wallahi sai Allah ya kwashe Aikin shi duka yaba mijinta ''inalillahi wa'inna ilaihir-raji'un". ka sani cewa daga lokacin da kai Zina da matar Aure to ka koma zero-zero wajen duk irin aikin da ka taɓa yi na lada tamkar ranar aka haife ka sai dai kuma dukkan zunuban da ka aikata suna nan akan ka har da na wannan Zinar da ka aikata da ita,


Ya Allah muna roƙon ka, ka sa chatting da muke yi a social media ya zame mana hanyar shiriya ba ta halaka ba mazan mu da matan mu, Masu yi kuma Allah yasa su tuba su daina, Allah ne masani.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post