Karanta Zafafan Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata Da ma'aurata:

Karanta Zafafan Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata Da ma'aurata:
 Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata Da ma'aurata:

Ina kallon ki ne tamkar tauraruwar nan da ta yi wa saura nisa. Ki huta lafiya abar Kaunata.


Zafafan kalaman soyayya masu dadi suna kara tabbatar da soyayya a tsakanin masoya. Yana da kyau saurayi da budurwa ko mata da miji su koyi Kalaman soyayya masu dadi da Jan hankali da za su dinga furtawa junansu. 


Hakan yasa a wannan topic na yau na kawo muku wasu daga cikin zafafan kalaman soyayya masu daukar hankalin masoya. Ga su kamar haka;

 

Zafafan Kalaman Soyayya Zuwa Ga Masoya 

Zuwa Ga Masoyiya Ta: Kin Yi Wa Sauran Mata Nisa: Son Ki ya mamaye dukkan zuciyata. Ina kallon ki ne tamkar tauraruwar nan da ta yi wa saura nisa. Ki huta lafiya abar Kaunata.


Bani Da Kamar Ki: Kalmomin da a kowane lokaci nake farin-cikin furta su gare ki su ne. Ko dan na san tini kin daɗe da sanin adadin yadda nake son Ki, nake kuma kaunar Ki sai dai kawai na ce bani da kamar KI. Burina a kullum bai wuce na ganin na mallake ki ba har abada. Wannan Kalaman soyayya ne masu zafi ga masoya. 


Kin Zamo Fitilar Zuciya: Na kan ji wani abu a cikin zuciyata, ba komai bane face fitila wadda ke kunnuwa a dukkan lokacin da na sanya idanuwana a cikin naki. Ina son Ki fiye da yadda alamun hakan ke bayyana a saman fuskata. Ki huta lafiya.


Kin Zamo Cikin Tunanina: Kina daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da su ba a rayuwata. Kin zamo cikin tinanina. Bana fatan zuwan wani abu da zai zamo silar rabuwarmu, ko da a ce mutuwa ce. Ina Son Ki masoyiya. Kalaman soyayya ne masu dadi ga masoya. 


Ki Kalli Samaniya: Ki kasance mai ɗaga kanki Ki kalli sararin samaniya a cikin kowane dare, kada ki firgita a lokacin da kika hango wata mai tsananin haske, ni ma na yi hakan kuma na samu ganin wata tauraruwa mai haske idaniya da kore damuwar zuciya wato ke. Ina Son Ki.


Ke Ce A Zahiri Kuma Ke Ce A Cikin Bacci Na: A kullum na kan kwanta da tinaninki, na kuma farka a cikin mafarkin a cikin soyayyar ki, na gan ki zaune kusa da ni, a cikin wani lambu ma'abocin tsintsaye da furanni. Tabbas a lokacin murmushinki ya fi komai jan hankalina, muryarki kuma ke samar da nutsuwata. Ki Huta Lafiya abar kauna. Kalaman soyayya na kwanciyar hankali. 


Ko Kin San Hakan Na Faruwa A Kansa Saboda Ke?: Duk inda ya tafi, ko me yake yi yana tinaninki da soyayyar ki. Ko bacci yake yi ko a farke yake, yana hasaso murmushinki. A dukkan lokacin da kika yi nesa da shi, wajen ganin fuskarki ba ya buƙatar hotonki. Karda ki yi tinanin wani ne na daban face ni. Ina Matuƙar son Ki kamar yadda kika daɗe da sanin hakan.


Kalaman Soyayya Zuwa Ga Budurwa 

Burina Ki Kusanta Da Ni: Da akwai wata ƙaya a cikin zuciyata, wadda ta kasance cikin sukana a dukkan lokacin da na tina tazarar da ke tsakaninmu. Da ma a ce zaki mayar da ni wani sashe na zuciyarki na tabbata da na samu sassauci cikin soyayyar ki. Abu mafi soyuwar furtawa a gare ni zuwa gare ki shi ne, Ina Son Ki. Kalaman soyayya na masu saka nishadi ga masoya. 


Kalmomi Sun Yi Kaɗan Wajen Bayyana Yadda Nake Son Ki: Masoyiyata, ina son na sanar da ke adadin yadda nake son Ki a cikin zuciyata, sai dai kuma, na rasa samun kalaman da zan yi amfani da su wajen bayyana hakan a gare Ki. Ina son ki. Ki kula min da kanki.


Kada Ki Ɗauki Hakan A Matsayin Almara: Da a ce a yau zan samu fukafukan tashi, na tashi izuwa sararin samaniya, na je na gano taurari, na sauko izuwa doron duniya, bana fatan Ki tsunduma cikin matsanancin mamaki a lokacin da na bayyana miki cewa kin yi kama da ɗayarsu wato Zara. Kalaman soyayya ne tsakanin masoya masu jan hankali. 


Kalaman Soyayya Daga Saurayi Zuwa Budurwa 

Zan Yi Rayuwar ƙunci Idan Babu Kai: A dukkan lokacin da ka furta baka so na, babu inda ya fi dacewa da na ci gaba da rayuwa a cikinsa face kabari, domin kuwa na san daga ranar duniya za ta zamo wajen zubar hawayena. Ina Son Ka.


Akwai Wani Sirri Cikin Idanuwanka: Rayuwata ta kasance rataye cikin tarkon soyayyar ka, ka ɗana kuma ya kama ni. A dukkan lokacin da na kalli ƙwayar idanuwanka, na kan ji wani shauƙi mara misaltuwa. Ina Son Ka. Kalaman soyayya ne dake birge masoyi. 


Kai Ne Abun Son Kallon Idaniyata: Ina cikin kewarka, ina cike da ɗaukin son ganin Ka, a cikin kowace rana son ka na lunkuwa a cikin zuciyata, fiye da yadda fatar bakina za ta iya furta hakan. Ka huta lafiya masoyi.


Bana Fatan Canjuwar Ra'ayinka A Kaina: Abu mafi tsanani wajen sanya zuciya a damuwa shi ne, ka samu wanda kake so shi kuma a lokacin ya faɗa a son wata. Bana fatan hakan ya kasance a tsakanina da kai. Ina Son Ka! Ina Son Ka!! Ina Son Ka!!! Masoyina. Wannan kalaman soyayya na ratsa zuciyar masoyi. 


Fatana Mu Kasance Tare Har Abada: So abu ne mai wahalar da zuciya da kuma sanya ta nishadi. Zan so ka kasance cikin bani kulawa domin gujewa faɗawa wahalar ta so. Ba zan taɓa canja ra'ayina a kan ka ba har abada. Ina Son Ka.


Kalaman Soyayya Na Miji Ga Matarsa 

Kin Haska Duniya Ta: Samuwarki a rayuwata ne ya koyar da ni har na san zahirin siffa ta SO. Sai bayan da muka yi aure na ƙara fahimtar soyayya ta gaskiya. Ina fatan mu kasance a tare da juna na tsawan rayuwa har zuwa gidan Aljanna. Ina matuƙar Son Ki matata. Amma a lokacin da na dawo gida za ki ƙara tabbatar da hakan. Hmm! Ina nan cike da zumuɗin son zuwa cin girkinki mai daɗi.


Ɗaya Tamkar Da Goma: Da akwai wata mace a cikin wannan duniya, wadda ta yi daban da sauran matan dake a gidajensu na aure. Ita ta kasance ta daban ce, halayanta kuma ababen so ne. Ba kowa bace face Ke, a saboda haka nake ƙara son Ki a kullum. Ki kula min da kan ki, har zuwa lokacin da zan dawo gida kulawarki ta dawo hannuna. Ina Son Ki Matata.


Kalaman Soyayya Daga Mata Zuwa Mijinta 

Shin Ko Ka Lura Da Hakan? Zuciyata ta riga ta saba da kai, ta yadda nake iya jin tamkar na zamo cikin jakarka a dukkan lokacin da ka tashi fita. Da tinaninka nake wuni idan ka fita, sai kuma ka dawo nake samun sukunin yin murmushi. Ina Son Ka Mijina. Wannan kalaman soyayya yana birge miji. 


Hm! Hmm!! Hmmm!!! Karda ka so ɗaya, kuma karda ka so biyu, amma dai ka ci-gaba da son ɗaya wadda ta mace a kan son ka. Mijina kai ne abun alfaharina da kuma 'ya'yana. Ina Fatan Dawowarka Gida lafiya.


Wannan Saƙon Zuciyata Ne Zuwa Ga Mallakinta: Kalmomi na kasancewa ma'abota sauƙi wajen furtawa a dukkan lokacin da SO ya kasance shi ne harshen furtawar. Zuciyata na yin haske a dukkan lokacin da muke tare, na kan shiga damuwa idan ka nesanta da ni. Duk da ka zamo mallakina amma zan so ka kasance mai kare min kanka daga harin da sauran mata zasu ke kawo maka a duk inda kake. A dawo lafiya.


Sako Mai Muhimmanci

Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. Don haka sai a kiyaye sosai.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post