Alamomin Yadda Ake Gane Mutum Ya Kamu Cutar Kanjamau HIV (AIDS)

Alamomin Yadda Ake Gane Mutum Ya Kamu Cutar Kanjamau HIV (AIDS)
Alamomin Yadda Ake Gane Mutum Ya Kamu Cutar Kanjamau HIV (AIDS) 


Akwai wasu alamomin yadda ake iya gane mutum ya kamu da cutar Kanjamau HIV, (AIDS) 


Cutar kanjamau ciwo ne da kwayoyin cuta na virus suke kawowa. Wadannan kwayoyin cuta ba kamar na bacteria bane, domin su suna da wuyar sha’ani saboda hayayyafa da suke fiye da yadda wani magani zai yi musu tasiri. Ma’ana ana hayayyafar su suma ‘ya’yan suna kara hayayyafa kamar kiftawar ido.


Wannan shine a ke kira da kwayar cutar HIV, domin kwayoyin su kan mamaye kwayoyin garkuwar jikin dan adam, sannan su haddasa wa jiki ciwon Aids, a sakamakon mutuwar wannan garkuwa ta jiki.


Yadda Ake Kamuwa Da Kanjamau (AIDS)

Binciken likitoci ya bayyana yadda ake iya daukar ciwon sannan sun tabbatar da ana daukar wannan ciwo ne ta hanyoyi guda hudu, hanyoyin sune kamar haka:


1. Saduwa da mai ciwon: 

Babbar hanyar da kanjamau ta fi yaduwa da shahara itace hanyar zinace-zinace. Idan an yi Jima'i da mai ciwon ko da sau daya ne, in dai har ruwa ya fito daga jikin mai ciwon, zai iya sakawa wanda bashi da ciwon ya kamu, musamman idan akwai miki (ciwo)ko da kuwa yankan gashi ne wanda ido ba zai gani ba ko kuma kurji a dai dai gurin saduwar ko kuma inda ruwan mai ciwon ya taba.


Za’a iya kamuwa da cutar ko da kuwa an sa kariya ta kwaroron roba (condom) domin kwayoyin sukan iya fita ta kananan kofofin jikin robar.


Domin sun fi kofofin duk wata kariya kankanta. To amma idan da kariya akan iya rage hatsarin kamuwa daga kaso dari (100) zuwa kaso casa’in (90).


Wannan ya nuna zina tana da mummunar illa ga rayuwar dan adam, domin babu tabbas din mutum zai iya kare kansa daga sharrin kanajamau (Aids) matukar ba zai bi dokokin Allah ba.


2. Karin jinni mai dauke da kwayar cutar: 

Karin jinni da ake yi wa wasu ba tare da an gwada jinin ba. Domin akwai masu dauke da wannan ciwo da dama, suna dauke da ciwon a jikin su ba tare da sun sani ba a dalilin sakankance da suka yi na amfani da kariya (condom) saboda kuskure ko kuma kin gaskiya. Anan wani zai ce; to shi sauro fa da yake zukar jinin mutane, ya dora wa wasu, me yasa ba ya sawa mutane cutar? Ga amsar nan, bincike ya nuna kwayar cutar tana mutuwane a cikin sauro sabanin malaria da take rayuwa a jikinsa.


3. Daga uwa zuwa jariri: 

Ita kuwa uwa takan iya bawa jaririnta ne tun yana cikinta, ko kuma lokacin haihuwa ko na shayarwa.


4. kayan kaifi: 

daga kayan kaifi ma yana faruwa a lokacin da aka yi amfani da reza, aska, kaho ko allura wadda mai kwayar cutar yayi amfani dasu.

Wannan ya tabbatar da cewa, ita dai kanjamau an fi kamuwa da ita ne ta hanyar zinace-zinace, domin ba’a iya kamuwa da ita ta hanyar taba jikin mai cutar kamar gaisuwa ko musabiha da dai sauransu.


Alamomin Yadda Ake Gane Ciwon Kanjamau.

Shigar kwayar cutar jikin mutum ba dolene ya zo da wata alama ba, domin mutum zai iya kaiwa shekara goma (10) yana dauke da cutar ba tare da ya san cewa ita ce a jikin sa ba.


Amma wannan ya fi faruwa ga mutane masu karfin garkuwar jiki. Amma wasu mutanen marasa karfin garkuwar jiki ko yara kanana, watanni ne kawai kwayar zata yi ajikin su, sannan su fara nuna alamu.


Alamun sune za’a ga yana ta rama wata da watanni bayan kuma yana cin abinci kamar yadda kowa yake ci, ko gudawa (zawo) wanda yaki jin magani na tsawon makonni, ko tari wanda ya ki jin magani tsawon makonni, domin yawanci tarin TB ya fi kamasu. Duk da cewa tarin TB shine babbar alamar ciwon kanjamau a irin kasashen mu. Amma bai zama dole kuma mai tarin TB ya zama yana da ciwon ba.


Wadannan manyan alamu, amma akwai kuma sauran alamu da yawa. Misali duk wani ciwo da yaki ci yaki cinyewa, zai iya kasancewa sanadinsa shine kanjamau.


A wani bincike da kungiyar lafiya tayi a majalisar dinkin duniya (WHO) ta gudanar a shekarar 1993, sun yi hasashen cewa zuwa shekara ta 2000 za’a iya samun mutane  miliyan ashirin zuwa abin da yayi sama na wadanda za su kamu da wannan cuta daga kowane bangare na duniya. Suka ce amma a yankin nahiyar afika (Africa) cutar ta fi saurin yaduwa saboda yawan zinace-zinace barkatai.


Amma kasar amurka (America) da sauran kasashen turai cutar tana yaduwa ne ta hanyar luwadi da madigo da kuma “yan kwaya masu yiwa kansu allurar maye haka kawai.


Hanyoyin Yadda Za'a Iya Yin Kariya Daga Cutar Kanjamau.


1. Kamewa daga barin zina

2. Gwajin jini ga wanda za’a aura kafin a daura aure, matukar ba'a yarda da shi/itaba. Kuma a nuna takardar shaida kafin a daura auren. 

3. A tabbatar an tafasa kayan kaifi, kamar na wanzamai ko na mai yankan farce ko an kona su da wutar lighter ko kuma a wanke da ruwan bleach kafin ayi amfani dasu.

4. Yawaita zuwa cibiyoyin gwaji don sanin matsayin mutum ya na taimakawa wajen rage yaduwar ciwon matukar mutum bai yarda da kansa ba.


Wadannan sune kadan daga cikin alamomin yadda ake gane mutum ya kamu da cutar kanjamau da kuma hanyoyin yadda ake kare kai daga kamuwa da cutar.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post