Yadda Ake Gane Boka |
Alamomin Yadda Ake Gane Boka Da Irin Halayyar su
Boka Da Malami akwai bambancin yadda ake iya gane su. Sai dai ba duka mutane ne kan iya bamhance tsakanin Boka da malami ba. Haka yasa muka tattaro muku wasu alamomi na yadda ake iya gane Boka kamar haka;
Alamomi Yadda Ake Gane Boka
Daga cikin alamun yadda ake gane Boka shine ya tambayi sunan marar lafiya da sunan mahaifiyar sa
- Idan Boka ne yana neman a kawo masa wani abu na marar lafiya (tufafi, hula, hankici da makamantansu)
- Ya nemi a kawo masa wata dabba da zai yanka, kuma ya fadi siffofinta da kuma kalar ta.
- Idan Boka ya umarci marar lafiya, ya kauracewa mutane a wani daki da rana bata shiga
- Ya nemi marar lafiya kada ya taba ruwa tsawon wani lokaci (sun fi cewa kwana arba'in)
- Ya bawa marar lafiya wasu abubuwa da zai binne a cikin kasa
- Ya rinka fadar wasu maganganu da ba'a fahimtar su
- Boka daga zuwa wajen sa ya fadawa marar lafiya sunansa da garinsu da matsalar da ta kawo shi.
- Ya bawa marar lafiya wata takarda wadda aka rubuta wadansu haruffa a rarrabe
Wadannan sune wasu daga cikin alamomin yadda ake gane boka, domin shi duk abubuwan da zai yana sabawa umarnin Allah ne. Da fatan al'umma kun ilimantu daga abubuwan da kuka Karanta.
Tsokaci:
Ku sani Allah baya son shirka, duk wanda yaje gurin boka ya kuma yadda ya yi aiki da maganar sa ya kafirce wa abinda aka saukarwa da Manzon Allah (SAW), duk wanda yaje ya ji maganar sa baza'a karbi sallan sa ba ta tsawon kwana arba'in.
Idan kinsan/kasan akwai matsala ki/ki gaugauta tuba zuwa ga Allah.