Abubuwa 6 Da Ake Buƙatar Ma'aurata Su Yi Bayan Kwanciyar Aure |
Yana da kyau ma'aurata su riƙa yiwa junansu godiya a duk bayan Kwanciyar aure, saboda yadda kowane cikinsu ya bada tasa gudunmawar wajen daɗaɗawa junansu
Ba wai kawai kwanciyar aure bane yake baiwa ma'aurata ƙarin soyayya da kusantar juna ba. Akwai wasu halaye da ɗabi'un da ma'aurata idan suna yiwa junansu duk bayan ko wani kwanciyar aure tofa a kullum za su ƙara danƙon soyayyar a zaman su na aure.
A wannan darasin zamu kawo muku abubuwa 10 Da suka dace ma'aurata su kasance suna yi a duk bayan kammala jima'i a zamantakewar auren su. Ga abubuwan kamar haka;
1: Yiwa Juna Godiya: yana da kyau ma'aurata su riƙa yiwa junansu godiya a duk bayan Kwanciyar aure, saboda yadda kowane cikinsu ya bada tasa gudunmawar wajen daɗaɗawa junansu.
Hakan nan kuma kowannensu ya kashe sha'awarsa ne ta halattacciyar hanya a dalilin aure. Wannan yasa yiwa juna godiya duk bayan jima'i yana da kyau da ƙara soyayyar juna.
2: Tsaftace Al'auran Juna: Yana da kyau duk bayan kammala jima'i ma'aurata su tsaftacewa junansu, kamar jikin su kamin su shiga wanka. Mace ta tsaftace dukkannin inda jikin mijinta ya ɓaci. Haka shi ma mijin ya tsaftace mata nata. Bai dace ba da zaran ma'aurata sun gama jin daɗin kwanciyar aure sai kowa ya shiga gyara jikinsa da kansa. I
3: Yin Wanka Tare: Bayan kammala jima'i yana da kyau ma'aurata su shiga su yi wanka tare. Su cuccuɗa junansu. Hakan yana ƙara danƙon soyayya matuƙa ga ma'aurata.
4: Ciyar Da Juna: Mafi yawan mutane suna son cin abinci bayan kammala jima'i. A irin wannan ya dace koda guda baida sha'awar ci, to ya zauna tare da gudan yana ciyar dashi ko suna ciyar da juna. Wannan salo na soyayya bayan jima'i yana ƙara kusantar ma'aurata.
5 Tattaunawa Akan Jima'i: A wannan lokacin yana da kyau ma'aurata su taɓa batun kwanciyar aure da suka kammala a Lokacin. Idan akwai abunda aka yi wa guda da bai gamsar dashi ba sai yayi magana. Idan kuma dukkaninsu sun samu gamsuwar da suke buƙata sai su kambama juna tare da jaddadawa juna salon kwanciyar da suka fi buƙata ko kuma Wasannin Motsa Sha'awa.
Irin wannan hiran yakan baiwa ma'aurata daman gano abunda suke so da kuma abunda suke ki a lokacin jima'i.
6: Kwanciya Tare: bayan kammala jima'i yana kara soyayya a tsakanin ma'aurata. Wasu ma'auratan idan sun yi kwanciyar aure sai kaga sun ware da junansu. Hakan yana nuna babu wata soyayya dake tsakanin su. Kwanciya tare na kara tabbatar da kaunar juna tsakanin ma'aurata.
Waɗannan sune daga cikin abubuwan da ake buƙatar ma'aurata su dinga yi a tsakanin su idan sun kammala kwanciyar aure. Da fatan kun ilimantu daga cikin abubuwan da kuka karanta.