Yadda Wani Dagaci A Jigawa Yaiwa Yarinya Fyade Har Ya Shafa Mata HIV

Yadda Wani Dagaci A Jigawa Yaiwa Yarinya Fyade Har Ya Shafa Mata HIV

Yadda Wani Dagaci A Jigawa Yaiwa Yarinya Fyade Har Ya Shafa Mata HIV 


Yadda Wani Dagaci A Jigawa Yaiwa Yarinya Fyade Har Ya Shafa Mata HIV 


Wani Dagaci da ake zargi da cin zarafin yarinya ta hanyar yi mata fyade da kuma shafa mata cuta mai garkuwar jiki wacce aka fi sani da HIV ya gurfana a gaban kotu. 


Dagacin wanda aka ce shine mai unguwar Dangulam dake yankin Karamar Hukumar Gwaram a jihar Jigawa ya yiwa matashiyar fyade wanda har ta samu juna biyu. 


Wata takarda da Ma’aikatar Shari’a ta jihar ta aike wa Sakataren Masarautar Dutse, “Nan gaba za a gurfanar da mai unguwar Dan Gulam kan zargin da wani magidanci ya kawo wa Antoni-Janar cewa basaraken ya yi wa ’yarsa fyade dauki ciki kuma ya sa mata kwayar cutar HIV.”


Don haka ta bukaci Majalisar Masarautar Dutse ta dauki matakin da ya dace gabanin gurfanar da wanda ake zargin a matsayin basarake.


Wasikar, dauke da sa hannun Kabiru Abdullah Esq, ta ce bayan samun korafin ne Antoni-Janar na jihar ya bukaci ’yan sanda su gudanar da bincike kan lamarin.


Da farko wanda ake zargin ya shaida wa ’yan sanda cewa ya yi karar yarinyar da mahaifinta a Babbar Kotun Musulunci da ke Gwaram bisa zargin zubar masa da kima.


Da jin haka ne kwamihinan shari’ar ya bukaci a dawo da lamarin gabansa, inda ya kara umartar sashen binciken manyan laifuka na ’yan sanda su binciki duka bangarorin da ke rikicin.


Wasikar ta ce, bayan bincike ’yan sanda suka tabbatar da zargin da ake wa mai unguwar, shi ne, “Antoni-Janar ya sa in sanar da Mai Martaba, don guje wa gurfanar da wanda ake zargin a matsayin basarake a masarautar.”


Iyayen yarinyar dai na rokon kungiyoyin kare hakki da su sanya baki cikin lamarin domin ceto rayuwarta da kuma sama mata adalci.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post