Wani mutum ya hadu da ajalinsa yayin gwajin maganin Bindiga a wajen Boka

Yadda wani mutum ya hadu da ajalinsa yayin gwajin maganin Bindiga a wajen Boka
Yadda wani mutum ya hadu da ajalinsa yayin gwajin maganin Bindiga a wajen Boka 


Wani mutum ya hadu da ajalinsa yayin gwajin maganin Bindiga a wajen Boka 


Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa an harbe wani mutum a jihar wajen gwajin maganin bindiga daga wani Boka wanda ake zargin shi ne ya bai wa mutumin maganin bindigar sannan kuma ya harbe shi, tare da wasu mutane biyu yayin da sauran waɗanda ake zargi suka gudu.


Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Ahmed Wakil ya bayyana cewa sunan wanda aka harba shi ne Muhammadu Ali, mai shekara 43, wanda aka kai shi Asibiti, sai dai an tabbatar da mutuwar sa a lokacin da suka isa.


Wakil yace za'a a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike,  ya kuma gargadi jama’a da su guje wa irin waɗannan abubuwa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post