Siffar Yadda Ake Yin Wankan Janaba A Koyarwar Musulunci

Siffar Yadda Ake Yin Wankan Janaba A Koyarwar Musulunci
Siffar Yadda Ake Yin Wankan Janaba A Koyarwar Musulunci 


Siffofin Yadda Ake Yin Wankan Janaba A Koyarwar Musulunci 


Ko kunsan siffar yadda ake yin wankan Janaba a muslunce? Da yawa daga cikin samari maza da mata ba su san yadda ake yin wankan Janaba ba, ba iya samari ba har da manyan mutane wanda suke da shekaru ba su iya wankan janaba ba. 


Shi dai wankan Janaba ya kasu kashi (2)


(1) Siffatul Kamalah

(2) Siffatul Ijza


Sifatul Kamalah 

Yadda ake yin wankan janaba na Sifatul Kamalah. Idan mutum zaiyi wankan janaba  na farko zai gudanar da wankan kamar haka:


1- ya wanke duk inda maniyyi ya taɓa jikinshi.

2- ya ƙudurta niyya a zuciyanshi.

3- yayi alwala, idan yazo kafafunshi sai yabarsu kar yawanke.

4- ya ɗebi ruwa ya zuba a kanshi sau uku ya tabbata ruwan ya shiga fatan kanshi, sai ya wanke kan baki ɗaya sau uku.

5- ya zuba ruwa ajikinshi ya fara da gefenshi nadama sa’annan gefen hagu

6- sai ya game jikinshi da ruwa gabaki ɗaya.

7- sai yawanke kafafunnshi da ya bari yayin alwala.

Wannan itace sifa cikakkiya ta wankan janaba.


 Siftul Ijza

Yadda ake yin wankan Janaba  ta siftul ijza  shine kamar haka:


1, Mutum bayan ya wanke maniyyi da yabata mishi jiki,

2, ya ɗebi ruwa ya kwarara a jikinshi baki ɗaya ya tabbata ruwan ya game jikinshi baki ɗaya, sai yasa ruwa a baki ya kurkura yashaƙa a hanci yaface shikenan.

3, Ana iya buɗe shawa ko a faɗa kogi ko tafki da niyyan WANKAN JANABA idan an fito a kurkura baki a shaƙa ruwa, hakan ya wadatar.


Wannan sune hanyoyi guda biyu na yadda ake yin wankan janaba a tsarin koyarwar musulunci. kuma dukkan sifofinnan za’a iya yin Sallah dasu ba matsala matukar baiyi abinda zai war-ware masa alwala ba, Wallahu a'alam. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post