Amfanin Muruci Ga Mata Da Maza

Amfanin Muruci Ga Mata Da Maza
Amfanin Muruci Ga Mata Da Maza 


Amfanin Muruci Ga Lafiyar Mace Da Namiji Da Hanyoyin Da Ake Yin Amfani Dashi 


Amfanin muruci yana da yawa musamman ga maza da mata, yana yin tasiri wajen inganta lafiya, dadin jima'i da kuma lafiyar jiki. Muruci ana iya cinsa danye kuma ana iya dafawa a ci. Za mu bayyana muku amfanin muruci ke yi a jikin mace da namiji. 


Masana sirrin mata sun tabbatar da cewa ya danganta da yanda mace take sha'awar cin murucin, misali idan mace bata sha'awar muruci koda tana yawan cinsa babu abinda zai kara mata amma idan tana sha'awar cinsa to bincike ya nuna yana karawa mace dandano a yayin Jima'i, kuma yana saka mace juriya wannan babu tantama akai.


Shi kuma namiji yana iya cin danyen murucin, amma fa kada ku zata yanada dadi wajen cin danye, daurewa akeyi a ci domin yana tasiri sosai ga lafiyar namiji. 


Sannan ta wani bangaren idan bazaka iya cin danyen murucin ba, tun yana danyensa zaka yanyanka shi ka barshi ya bushe sai a samu kanunfari da citta a hada wuri guda sai a daka, a tankadeshi a rinka zuba kamar cokali daya a cikin shayi da zuma itama cokali daya amma shayin babu madara kuma ana sha kullum sau daya. Shima wannan yana karawa namiji karfi sosai, dan zaka iya fada da kowa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post