Yadda Hukumar Hisbah ta hukunta yan Daudu masu shigar mata Kano - Android Pols

Yadda Hukumar Hisbah ta hukunta yan Daudu masu shigar mata Kano

Yadda Hukumar Hisbah ta hukunta yan Daudu masu shigar mata Kano 


Yadda Hukumar Hisbah ta hukunta yan Daudu masu shigar mata Kano 


Kotun shari'ar addinin musulinci dake zaman ta a hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta yankewa wasu matasa yan Daudu hukunci bayan sun yi shigar mata dan yin rawar karya Ƙugu a wajen bikin uban gidansu.


Alƙalin kotun mai shari'a Malam Sani Tamim Sani Hausawa, ya samu matasan yan Daudun da laifin bayan an karanto musu ƙunshin tuhumar da ake yi musu, inda nan ta ke suka amsa, sai dai sun roki kotun ta yi musu sassauci.


Mai shari'ar ya yanke musu hukuncin daurin watanni uku ko zabin biyan tarar Naira dubu goma-goma kowannen su, tare da yi musu Bulala goma-goma.


Mukaddashin kwamandan hukumar Hisbah na jihar, Dr. Mujahiddin Aminuddin Abubakar, ya bayyana cewa, hukumar ba zata gajiya wajen dakile ayyukan badala ba, domin aikin hukumar shi ne yin hani da aikata mummuna tare da kiran aikata kyakkyawa.


Kalli bidiyon yadda aka zane yan Daudu 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post