TSAKANIN ISRA’ILA DA FALASDINU: Salsalar Rikicin Da Ba Ya Karewa Har Duniya Ta Tashi

TSAKANIN ISRA’ILA DA FALASDINU: Salsalar Rikicin Da Ba Ya Karewa Har Duniya Ta Tashi
Salsalar Rikicin Da Ba Ya Karewa Har Duniya Ta Tashi


TSAKANIN ISRA’ILA DA FALASDINU: Salsalar Rikicin Da Ba Ya Karewa Har Duniya Ta Tashi


Dandazon mayakan Romawa sun ci Yahudawa (Bani Isra’ila) da yaki shekaru 70 bayan Annabi Isa (AS), wato shekaru 500 kenan kafin haihuwar Annabi Muhammadu (SAWW). Ba cin su da yaki kadai su ka yi ba, Romawa sun fatattaki Yahudawa daga Jerusalem, su ka warwatsu cikin duniya.


Romawa sun ruguza babban ginin bautar Yahudawa da sauran wuraren bautar su.


Bayan zamani mai tsaro su kuma mahara dakaru na Byzantine daga Constantinople, Turkiyya kenan a yanzu, su ka darkaki Romawa da yaki har su ka fatatake su daga Jerusalem.


Jerusalem na cikin yankin da ake kira Levante, wanda a yanzu ya hada da Syria, Lebanon, Falasdinu, Jordan, Isra’ila (Jerusalem ta wancan lokacin), wani yankin Turkey, Greece, da Gabacin Libya.


Jihadin Musulunci Bayan Wafatin Annabi (SAWW):


Yankin Levante da mashahuriyar Daular ‘Mesopotamia’, wato su Iraqi kenan a yanzu da Babyloniya da mayakan Akkadiya da Sumeriyawa sun fada hannun Musulmi a zamanin Halifa Umar bin Khattab (RA).


Haka ita ma Daular Fasha wato Iran a yanzu da Sham da Alkahira da Askalan da sauran biranen da su ka hadu su ka yi Masar da Afrika ta Arewa da Jerusalem da Falasdinu, duk sun fada hannun Musulmi a zamanin Halifa Umar (RA).


Nasarar Musulmi A Falasdinu:


Wannan yaki kusan shi ne gumurzun da a baya Musulmi ba su taba yin yaki mai tsanani irin sa a baya ba. Ya faru shekaru uku ko hudu bayan wagatin Annabi (SAWW), 636 A.D.


A lokacin dakarun Musulmi sun yi galaba kan dakarun Byzantinawa a karkashin kwamandan su Heracluus, inda su ka kwashi kashin su a karkashin kwamandan Musulmi Khalid bin Walid.


Dakarun Musulmi sun ci Falasdinu da Jerusalem da yaki, su ka murkushe Byzanrinawan da su ka kori Romawa a Jerusalem. Su kuma Romawa dama su ne su ka kori Yahudawa, fiye da shekaru 500 kafin Musulmi su ci yankin da yaki kenan. Kamar yadda aka bayyana a farkon wannan rubutu.


Yadda Halifa Umar (RA) Ya Datsa Falasdinu:


An raba Falasdinu gida biyu: Akwai yankin ‘Jund al-Urdunn, wato Jordan, wanda kunshi Galilee da Acre.


Akwai kuma Jund Filastin, wato Falasdinu, inda aka yi mata hedikwata a Lydda ko kuma (Lod/Lud).


Jerusalem kuwa can ne aka gina Masallacin Asqa, wato Baitil Muqaddis, masallaci na uku mafi daraja ga Musulmi. Ko da yake akwai tarihe-tarihen da su ka nuna an gina masallacin tun shekara 40 bayan da Annabi Ibrahim (AS) ya gina Dakin Ka’aba a Makkah


Litattafan tarihi sun nuna cewa Musulmi sun amince Yahudawa su koma su zauna bayan korar su da aka yi fiye da shekaru 500 daga kasar su, Jerusalem.


Halifa Abdulrahman bin Marwan, wanda ya hau Halifancin Daular Musulunci a karashin mulkin Banu Umayyah, ya sa aka gina hasumiyar nan da ake kira ‘Dome of the Rock’ (Qubbat al-Sakra) a Jerusalem.


Bayan kawar da mulkin Daular Banu Umayyah a Sham cikin shekarar 750 A.D, Daular Abbasiyawa ta kafa mulki ita kuma Bagadaza (Iraq).


Yayin da Daular Fatimiyyah ta kafa mulki a Afrika ta Yamma a karkashin Halifa Hakim, ta mamaye Masar da Palasdinu. Ita wannan Daula wadda ta mabiya Shi’a ce, ta rika kwankwatsar Kiristoci da Yahudawa. Ta rusa babban Cocin Jerusalem cikin 1009 A.D.


‘Crusade’: Yakin Ramuwar Gayyar Kiristoci A Kan Kasashen Musulmi:


Bayan shekaru 90 da rusa babban Cocin Jerusalem, wasu daulolin Faransa sun fara kwakkwaran shirin kwato wasu kasashen da musulmi su ka mamaye da kuma kai na su sabbin hare-haren, wato ‘crusade da ‘reconquesta’. Kalmar ‘reconquesta’ yaren Sifananci (Spain) ne. Za mu dawo kan wannan yakin a Spain.


Dakarun ‘crusade’, wato yakin kisan kiyashin da Kiristoci su ka yi wa musulmi a duniya, sun tashi rundunonin yaki daban-daban a cikin 1094 A.D bisa tsare-tsaren Sarki Urban III na Faransa.


Dalilan Yake-yaken ‘Crusade’ A Jerusalem Da Falasdinu:


1. A kasashen Turai an rinka baza labarai da hikayoyin karya da gaskiya dangane da zarge-zargen gallazawar da Musulmi ke wa Kiristoci a yankin ‘Levante’, yankin da ya hada da Jerusalem da Falasdinu.


2. Turawan Yamma masu zuwa ziyara Jerusalem sun rika komawa gida su na baza labaran ana gallaza masu idan sun je Jerusalem da Falasdinu.


3. Akwai dalili na tsananin son yin ramuwar-gayya.


4. Akwai masu tsantsar akidar addinin Kiristanci da ke ganin cewa idan su ka yi ramuwar-gayya, to su ma ‘jihadin Kiristanci’ kenan su ka yi.


5. Masu tsantsar ra’ayin Kiristanci na ganin kwato Jerusalem da Falasdinu a hannun Musulmi zai sa su samu tsira a gobe kiyama.


6. Akwai dalili na jin haushin yadda aka ci garin Antioch da yaki, gari mai dimbin tarihi ga Kiristoci, inda Peter da Paul zu ka rayu.


Yakin Kwace Jerusalem Daga Hannun Musulmai:


Dakarun Kiristoci ‘yan ‘Crusade’ sun samu galabar kewaye Jerusalem cikin watan Yuni, 1099. Sun ci birnin da yaki a ranar 15 Ga Yuli, 1099.


An kashe dubun-dubatar Musulmai a Jerusalem, har ta kai ga masu bada labaran hikayoyin da ba su inganta ba sun rika bada labarin cewa jinainan Musulmai ya rika kwaranya a kasa har sai da zurfin sa ya kai kafar wanda ke kan doki na iya tabo jinin da ke gudana a kasa. Wato jini ya kai daidai gaban doki kenan.


Amma dai wannan labari duk hikayoyi ne kawai na karin-gishiri, da ke nuna irin munin barnar da aka yi.


Yakin Shekarar 1187: Salahuddeen Ayyuby Ya Kwato Jerusalem Daga Hannun Kiristoci, Ya Sake Gina Masallacin Baitil Muqaddis.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post