Abubuwan Dake Jawo Yawan Sha'awa

Abubuwan Dake Jawo Yawan Sha'awa

Abubuwan Dake Jawo Yawan Sha'awa 

   

Abubuwan Dake Jawo Yawan Sha'awa 

   

Duk da sha'awa halitta ne kamar yadda kowa ya sani, da akwai kuma wasu halaye, dabi'un da sukan iya jawowa mutum ya kasance a kullum cikin sha'awa.


Kamar komai, shima yawan sha'awa na iya jefa mai yinsa cikin matsalolin dake iya cutar da shi a dabi'unsa na yau da kullum. Yawan Sha'awa ke sa maza suke yiwa yara kananu fyade, yawan sha'awa ke jefa wasu ma'aurata maza neman matan banza. Karfin sha'awa ke sa wasu matan auren neman maza. 


Ga wasu kadan daga cikin abubuwan dake jawowa maza da mata karfin sha'awa na Jima'i.


1:Hormones: Sune kwayoyin halittar mutum suma kamar yadda muka yi bayani a farkon shinfidar mu, su masu irin wananna kwayar halittar a kullum a cikin bukatuwa suke na Jima'i.


2: Abinci: Akwai wasu nau'in ci maka da suke sa sha'awa da zarar mutum ya ci irin wannan abincin zai ji sha'awa ya taso masa.


3: Giya Ko Kwaya: suma sukan jawowa mutum yawan sha'awa na Jima'i. Akwai wasu barasar da komai rashin  sha'awar mutum yana sha nan take sha'awa zai kama shi. Kamar yadda ake da wasu kwayoyin maganin da suma suke kara sha'awa kuma ba saboda hakan aka yi su ba.


4: Tashen Balaga: A lokacin ne yara suke shiga hadarin neman mata, luwadi da madugo. A lokacin da yara suke wannan rukunin a kullum cikin sha'awa suke musamman ma 'ya'ya mata. 


5: Al'ada :  kafin lokacin al'ada, ana yi da kwanaki uku bayan mace ta gama al'ada a wannan lokacin mata suna shiga wani irin  sha'awa da basu samun kansu idan ba irin wannan lokacin bane.


6: Ciki: Yana yin jikin mace na sauyawa a lokacin da suke da ciki. A wannan lokacin mata sha'awar su yana karuwa sosai na Jima'i fiye da kafin ciki ya shiga.


7: Mafitsara: Mutanen dake da lafiyan mafitsara ko budaddiyar mafitsara suna da yawan sha'awa fiye da wadanda ba hakan suke ba.


8: Hira Ko Kallo: Hira musamman irin na batsa ko kallon hutuna ko bidiyon batsa. Wadannan abubuwan biyu da zaran za a yiwa mutum wannan hiran  ko yayi kallon a duk lokacin da ya samu kansa a hakan sai yaji bukatuwa ya kama shi.


9: Kwanciyar Hankali Da Wadata- Duk mutumin da ya samu kansa cikin kwanciyar hankali da Wadatuwa na yau da kullum zai kasance cikin sha'awa.


10: Lafiya: Mutumin dake da lafiya na jiki dana kwakwalwa zai kasance cikin sha'awa.


Wadannan sune kadan daga cikin abubuwan dake haddasa yawan sha'awa ga maza da mata, da fatan kun amfana daga abubuwan da kuka Karanta. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post