Kalli Hotunan Yadda Aka Gudanar Da Maulud Annabi Muhammadu (SAW) A Bauchi Na 2023Kalli Hotunan Yadda Aka Gudanar Da Maulud Annabi Muhammadu (SAW) A Bauchi Na 2023 


Fitaccen malamin addini kuma jigo a darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya gudanar da Mauldin Annabi Muhammad SAW a birnin Bauchi wanda dubban jama'a daga sassan Nijeriya suka halarta. 


Taron Mauludin an gudanar dashi a filin wasa na Abubakar Tafawa Balewa dake babban birnin Jihar Bauchi. Manyan malaman darikar Tijjaniyya sun halarci taron Mauludin tare da yin bayani akan tarihin Annabi Muhammad SAW. 


Taron Mauludin an saba gudanar da shi duk shekara karkashin jagorancin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.


Happy Maulud

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post