An Gano Ashe Ganduje Ne Yai Silar Janye Sunan Maryam Shetty Daga Cikin Jerin ministoci

 

Tsohon gwamnan jihar Kano da ke Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje shi ne silar janye sunan Maryam Shetty daga jerin sunayen mutanen da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ke son nadawa ministoci, yayin da ya maye gurbinta da Dr. Mariya Mahmoud Bunkure kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya bankado.


Jaridar ta rawaito cewa, wani babban jami'i a fadar shugaban kasa ne ya cusa sunanta cikin jerin sunayen ministocin na Tinubu, yayin da fadar ta yi zaton cewa, da sanin Ganduje aka bada sunan Maryam daga jihar Kano.


Makusantan Ganduje sun shaida wa Daily Trust cewa, babban dalilin da ya sa Ganduje ya nuna karfin iko har aka sauya Maryam da Bunkure shi ne cewa, ba ta cikin mukarraban siyasar tsohon gwamnan, sannan ta yi shura wajen sukar manufofinsa a lokacin da yake gwamna.


Bugu da kari, Shetty na da kusanci sosai da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi, inda har ta yi ta caccakar gwamnatin Ganduje kan yadda ta sauke Sarkin daga karagar mulki, abin da wasu majiyoyi suka bayyana a matsayin daya daga cikin dalilan janye sunanta.


Daily Trust ta rawaito cewa, shugaba Tinubu ya yi matukar mamaki bayan ya samu labarin cewa, ba Ganduje ba ne ya gabatar da sunan Shetty, inda mutanen da suka zabe ta suka nuna wa shugaban wani hoto da ta dauka da tsohon gwamnan don nuna cewa, tana tare da shi.


Tuni Shetty ta rungumi wannan sauyin da hannu biyu-biyu, tana mai cewa, haka Allah ya tsara, yayin da kuma ta yi wa gwamnatin Tinubu fatan alheri gami da jinjina.


Tun lokacin da aka sanar cewa, tana cikin jerin mutanen da Tinubu zai nada ministoci a gwamnatinsa, 'yan kasar musamman daga yankin arewa suka yi ta tafka muhawara game da kwarewarta ko kuma cancantarta, inda wasu suka taya ta murna, yayin da wasu kuma suka ce sam ba ta cancanci wannan mukamin ba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post