Wani magidanci a jihar Katsina ya saki matar sa mai shekaru 14 saboda ta bar wani likita ya karbi haihuwar jaririn da ta haifa.
Matashiyar ta samu rikitacciyar haihuwa kuma an garzaya da ita zuwa asibiti inda babu wata ma’aikaciyar jinya a kasa da za ta karbi haihuwar. Sakamakon haka ma’aikacin likitanci namiji daya tilo da ya samu halartarta a lokacin nakuda, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar aurenta.
Dr Fatima Adamu wacce ita ce darakta walwalar mata ta bayyana hakan a ranar Alhamis a yayin da take tattaunawa da manema labarai.
An bayyana cewa matashiyar takes haifi jaririn cikin lafiya mijin yayi murna lokacin da ya samu labarin matarsa ta haihu cikin kashi lafiya hakan yasa ya garzaya asibitin, sai dai bayan ya gano namiji ne ya karbi haihuwar nan take ya saki matarsa.