Kimiyya da camfe-camfe da ke tattare da bishiyar kuka a Afirka
Bishiyar Kuka (Baobab), bishiya ce da ta yi fice sosai a Nahiyar Afirka, takan tsiro a yankunan birane da karkara har ma a dazuzzuka, kuma ta na daga cikin mafi girma da dadewar bishiyoyi a duniya.


Idan hikima da kyawu da camfi da tarihi su na bukatar a ba su su na irin na kimiyyar sanin tsirrai, to fa ‘’Adansonia digitate", ko kuma katafariya, sannan tsohuwar bishiyar kuka da ta kafu ta kuma yadu a daukacin yankunan kudu da Saharar Afirka masu tsandauri, ta cancanci wannan girmamawa.


Bishiyar Kukar da ta samo asali daga nahiyoyin Afirka da Australia, ta na dauke da siffofin da su ka dace da yanayin Afirka, A tarihi, tare da kasancewa alama ga wasu al'adu da wasu suka yi Imani da su.


Bishiyar rayuwa ce ta hanyoyi da dama, da suka hada yanayin zamantakewa da al’adun dan adam da suka shafi tarihin dan Adam musamman a nahiyar Afirka da ta yi zurfi cikin kimiyya da camfe-camfe.


A cewar Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da yanayin hamada, bishiyar kuka "za ta iya rayuwa har tsawon shekara 3,000, kuma girman fadinta na iya kai wa mita 50 sannan tsayinta na iya kai wa mita 30."


Tana da ire-iren nau’i daban-daban har guda tara, shida daga ciki na iya tsirowa a yankin tsibirin Madagascar na Afirka, itaciyar kuka ta kasance abar nazari da bincike da kuma kwatance.


Daga cikin fitattun irin bishiyoyin kuka da ake da su a duniya, akwai Sagole Baobab na Afirka ta Kudu, wacce ta rike kambun duniya ta ‘Guiness World Record’.


A harshen Hausa ana kiran Baobab Kuka, Reniala a harshen Malagasy, da kuma Mbuyu da yaren Swahili.


Sunan bishiyar kuka Gouye Gui a harshen Wolof, da yaren Lingala kuma sunanta Zelo.


A cikin al'adun gargajiya wasu na kiran itaciyar kuka a matsayin jirkitacciyar bishiya. Yanayinta da ke a karkace, lamarin da ya sa tamkar tushenta na kokarin komawa sama.


Wani suna da ake kiran wannan bishiya da shi wanda ba a saba da shi ba shi ne, "cream of Tartar tree" - abin da ke nufin, rufaffen kwanson da ke jikin itaciyar.


Wannan kwanso ya kunshi wani sinadarin asid mai tsami wanda za a yi amfani da shi wajen hada madara da samar da sinadaran dafa abinci da yin burodi da kuma giya.


Bacewa a hankali


Kuka bishiya ce mai ban mamaki da ke girma a cikin birane, kauyuka da kuma gandayen daji. Itaciyar na cikin mafi girma kuma mafi dadewa a duniya.


Kama daga daga Madagascar da Afirka ta Kudu da Zimbabwe zuwa Senegal da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo da Nijeriya, jerin bishiyoyin na kuka sun kawata yanayin Afirka.


A kimiyyance, duk da itaciya ce mai laushi, an tabbatar da cewa kuka na jure cin wuta, “Sai dai in ta mutu ko kuma ta bushe.


Itaciyar ba ta ci da wuta'' a cewar Dakta Mustapha Karkarna, kwararre a fannin kula da gandun daji da ke Jami’ar Bayero ta Nijeriya yayin zantawar da TRT Afrika ta da yi shi.


"Kasancewar kuka wata dadaddiyar alama ce ko shaida a wurin da mutane ke zama, ta na da amfani da yawa wajen yin magani da sana'a.


A yanayi da ilimin muhalli, tana da daraja, hakan ya sa ba kasafai mutane su sare bishiyar kuka ba. Tsuntsaye na son bishiyar don irin kariyar da take bayarwa ga gidajensu da suke sakawa," in ji shi.


Sai dai a gargadin da Garba Sani, wani mai daukar shiri na bidiyo, ya ce a arewacin Najeriya, girman bishiyar kuka na bacewa sannu a hankali daga birane.


"Idan aka yi la'akari da irin griman gangar jikinta, ana ganin kuka a matsayin bishiya mai mamaye wuri musamman ta fannin masu gine-gine," in ji shi.


Sani ya koka kan yadda sabbin masu inganta filaye ke saurin yanke manyan bishiyoyin kuka, wanda ke haifar da raguwar samunsu a birane.


Nyasha Chibanda, haifaffen kasar Zimbabwe kuma kwararre a fannin ci gaban kasa da kasa, da ke zama a birnin Pretoria na kasar Afrika ta kudu, ya yi wani sharhi na daban.


"A lardin Masvingo da ke gabashin Zimbabwe, galibin bishiyar kuka na girma ne a yankunan karkara da ke da wurare masu fadi da yalwa. Mazauna wajen ba su ga dalilin da zai sa a yanke bishiyoyin ba."


Amfaninta da dama


Bayan kasancewarta wata alama ta al'adu a yankin Afirka, yaduwar kuka a nahiyar ya kasance abin fifiko saboda amfaninta na da mahimmanci sosai wajen zama matsuguni da abinci mai gina jiki da samar da waraka ta hanyar magani.


Baya ga wasu manya-manyan nau'i bishiyoyi da ake da su , bishiyoyin kuka na zama tamkar muhalli kasancewar tushen na zuwa kasa kasa ya rige kansa maimakon ya gangaro har ya iya lalata gine-gine.


Abdulkadir Musa, wani malami mai ritaya a garin Giade da ke jihar Bauchi a arewa maso gabashin Najeriya, ya yi kari kan muhimmanci da kuka take da shi ga muhallin yankunan.


Imani na gargajiya


Daga filayen noma zuwa gidaje, Kuka tana taimaka wajen takaita zaizayar kasa, kuma manoma ba sa ganin wani lahani a daga gindin bishiyar da ke zama inuwa da ke taimakawa amfanin gonaki.


Sani ya ambaci cewa a kasar Hausa sunayen wasu wuraren suna bin wata bishiyar kuka ce da ke asali a wajen ko kuma ta taba kasancewa.


“A tsohon birnin Kano, akwai wurare kamar Kuka Bulukiya da Kuka Uku, sannan akwai Kukar Atillo a garin Nahuce da ke Taura a Jihar Jigawa,” in ji shi.


A fagen al'adun Afirka, ana samun kuka a ko ina, wasu kuma sun ce ta mamaye ko ina. Ana yaba mata a wasu al'ummomi saboda yadda ake amfani da ita a gargajiyance wajen maganin wasu cututtuka.


Akasin haka, Kuka ta yi kaurin suna a wasu al'adun a matsayin bishiya mai mugun abu.


Wasu addinai a Afirka suna danganta nau'in da dubban tsafi kamar su bautar kakanni da addu'o'i da ake yi na tsubbu da, aljanu da dai sauransu.


A wasu al'ummomi kuwa ana daukar kuka a matsayin "bishiyar da ba a samun ta a cikin gari".


Juriya ga ko wanne irin yanayi


Al’adun Hausawa kafin zuwan addinin Musulunci, suna kallon bishiyar kuka a matsayin Wajen aljannu, kuma ana gargadin yara da su guji hawa ko wasa da bishiyar domin hatsarin shigar aljannu jikinsu.


Shahararriyar kungiyar bori ta raye-rayen Hausa ta na nuna kuka a yawancin ayyukanta.


Kirar bishiyar kuka na bayyana ne tamkar wata tsohuwar katangar tsaro. Bishiyar na iya zama matacciya bayan ta zubar da ganyenta, amma da sauri take farfadowa tare da bayyanar 'ya 'ya da ganyayyaki ta dawo rayuwa tare da kyalli.


Yanayin juriyar itaciyar kuka na ba ta damar cigaba da yin 'ya 'ya ko da kuwa ta fadi, muddin akwai wasu saiwoyi da ke manne a kasa.


''A bangaren bishiyar kuka da ke kai ruwa zuwa ganyayyakinta daga saiwowi da kuma wanda ke zukar ruwa zuwa ga saiwowin a hade suke, abin da ya sa karancin ruwa ba ya mata Barazana,'' in ji Dr. Mustapha Karkarna, tsohon shugaban shirin kula da albarkatun gandun daji na Jihar Kano a Nijeriya.


A cewar Dakta Karkarna, wasu nau'ukan cutuka dangin fungal ne ke haifar da ramuka a bishiyar kuka ba wani abune da ya saba hankalin dan adam ba.


Dakta Karkarna ya yi imanin cewa babban abin da ya sa ake camfi a kan kuka shi ne kasancewar bishiyoyin sun kasance cikin tsirrai mafi dadewa a duniya.


Bishiya daya ta na iya girmar mutum mafi tsufa a cikin al'umma gaba daya.


Don haka, ana daukar su a matsayin shaidun abubuwan da suka gabata, kuma su na da labaran da za su ba da na tarihin al'umma.


Yayin da bishiyar ke girmewa al'ummu, ta na dauke da alamar tsawon rai da hikima, abin da ya sa mutane suke mata fassarori masu nasaba da makabarta da kuma Aljanu.


Abinda ya sa a kan bayyana ta a matsayin wata alama ta mugun abu a cikin tatsuniyoyi da camfe-camfe.


Wata babbar barazana ga wanzuwar kuka duk da muhimmancinta a cikin yanayin nahiyar Afirka da al'adu daban-daban shi ne fadadar birane da fifita tsirrai baki fiye da nau'ukan na Afirka.


Amma kamar yadda masanin falsafar Jamus Friedrich Nietzsche ya ce, dole a sha wahala idan za a rayu, batun kawai shi ne a samu ma'ana cikin wahala.


Babu wani abu da watakila ya kwatanta wannan al'amari fiye da dadaddiyar bishiyar kuka da ta rayu a karnin da dan adam ke cigaba da bunkasa da kuma barnatar da kewayensa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post