Shin A Yawon(LALATA) Ake Samun Ciwon Sanyi (GONORRHEA)?
Ciwon sanyi (Gonorrhea) ciwo ne da ke addabar mutane a wannan lokacin, duk da har zuwa yanzu babu wani tsayayyen bincike da zai iya kiyasta adadin mutane da ke dauke da wannan ciwon a  Nigeriya a halin yanzu, amma akwai wani bincike na baya-baya da wasu masana suka fitar cewar: Kaso kusan ashirin da Takwas da digo daya (28.1%) na yan Najeriya suna fama da wannan ciwon. Wanda nima a irin cases da muke samu na kukan da mata ke yi da ciwon, za mu iya yadda ya kai haka koma muce ya fi, amma da ya ke ni ba Likita ba ce ba wai kaitsaye zan yi magana akan magani (Treatment) ko alamomin ciwon (Sing and symptoms)  ko hanyoyin kariya (Preventive measures) bane, duka da cewa a binciken da na yi na gano irin manyan illolin da wannan ciwon ke yiwa jama'a, a'a zan yi magana ne akan irin zargin da wasu ke yi game da hanyoyin da ake daukar wannan ciwon.


Wasu mutane ko wasu mata su kan zargin mazajensu da yawo idan har suka fuskanci suna dauke da wannan ciwon, yayin da a bangaran maza kuma suke kin bayar da hadin kai gurin ganin an nemi maganin wannan ciwo, wadannan abubunwa guda biyu suna taka rawa gurin ci gaba da bazuwar wannan ciwo a cikin al'umarmu.


Zan fara da bangaran mata, ku sani shi wannan ciwo na sanyi ba kawai ana daukarsa ta hanyar mu'ala tsakanin mace da namiji ba ne kawai, a'a ana iya daukarsa a bandaki wanda mutane da yawa suke shiga, kuma kasancewar maza sun fi mata fita su wuni a wajen ayyuka ko neman kudi hakan kan iya saka su samu wannan ciwo a bandakunan da suke shiga na tarayya ko kuma a gefen hanya da wasu kan yi bawali da sauran gurare.


Duk da akwai wadanda kan samu ciwon sanyi a gurin yawon tsakanin maza da ma matan gaba daya, amma kaitsaye ba za a ce dukkan wanda ke dauke da ciwon yana samu ta muguwar hanya bane, domin a halin da ake ciki yanzu na rashin tsaftar muhalli da yawaita mu'amala da bandakuna ana iya daukarsa fiye da mu'amala tsakanin mace da namiji, domin za ka ga har samari da yanmata da yara da ba su san menene mu'amala tsakanin mace da namiji ba kan samu ciwon ayi ta zaryar asibiti, wanda yawanci kuma ta wadancan hanyoyin ne da na ambata a baya, sannan ba wai maza ne kadai ke dauko wannan ciwon ba kamar yadda na fada a baya ba, suma matan na iya daukowa su sakawa maza ta hanyar hadakar bandakuna a gidajen biki da Suna ko makarantu da gurin aiki da dukkan wani guri na taruwar maza da mata, indai za a yi amfani da bandaki daya ana iya samun wannan ciwon.


A bangaran maza kuma wasu lokuta da dama idan ka je asibitoci za ka ga mata ne ke zuwa kawai ganin likita, idan aka bukaci mazajansu su zo wasu basa zuwa, wasu suna ganin ciwon kawai a jikin matan ya ke saboda su basa jin alamunsa ko kuma ki fadi irin na maza, yayinda wasu ke gudun kar a zargesu da yawo, wasu kuma suna da wasu matan da suke ganin me ya sa sauran matan ba su da shi sai ita kadai, don haka me ya sa za su biki gurin likita, sai dai abun da suka kasa sani idan mace tana da wannan ciwo to idan har mijinta zai yi mu'amala da ita to wannan ciwon yana jikin dukka sauran matan, watakila nata ne ya fi fitowa, idan kuma za ta shekara dubu tana magani idan har mijinta da kishiyoyinta (idan tana da su) ba su yi magani a lokaci daya a tare ba, to ciwon na ta ba zai taba warkewa ba har abada duk maganin da za ta yi, domin idan ta warke ita to yananan a jikin mijin zai dawo mata da shi, ko kuma idan ta yi maganin ita ta warke yana jikin sauran abokan zamanta zai dawo musu.


Kuma ba lallai wanda ciwon ya fara bayyana a jikinsa zai zama shine ya kawo ciwon ba, ya danganta da yanayin jiki, wani lokacin mijin ne zai dauko amma ya fara bayyana a jikin mace, wani lokacin kuma mace ce za ta dauko amma ya fara bayyana a jikin namiji, domin ciwon ya kan dauki lokaci a jikin wasu kafin ya nuna daga sati biyu zuwa watanni har ma fiye da haka.


Shi wannan ciwo na sanyi yana da illa kwarai da gaske, kwanaki mun tattauna da wani likita da ya ke mun bayanin irin yadda ciwon ke ci gaba da yaduwa a tsakanin al'umma, yana kuma haifar da matsaloli musamman ga ma'aurata, sannan shi wannan ciwo magungunnsa suna da tsada hakan kan kashe gwiwar wasu magidanta su ki bayar da hadin kai a nemi magani wani lokacin har sai ya yi illah, wani lokacin su kuma matan su kan boye ciwon idan suna jinsa a jikinsu saboda gudun kar miji ya ce suna da ciwon a samu matsala, ko su kuma mazan su boye su ki fadawa matansu don kar matansu su zargesu.


Daga karshe ina kira ga ma'aurata su dinga kyautata zato tsakaninsu, sannan idan ciwon ya bayyana a jikin daya ayi kokarin ganin an magance shi da gaggawa kafin ya kai ga illata jiki, sannan masu biye-biye suna dauko cutuka suna sakawa abokan zamansu daga maza har mata su ji tsoron Allah su daina, domin shi wannan yawon yana haifar da illoli da dama kamar shi wannan ciwon sanyi da ke addabar duniya a yanzu da babban ciwo mai cike da tashin hankali wato (HIV), sannan kuma ga azabar ubangiji da tashin hankali da mazinata kan hadu da shi a karshen rayuwarsu. Allah ya tsaremu baki daya amin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post