Wata mata ta kai karar mijinta bayan auren su da wata biyu, inda ta nemi kotu ta raba aurenta da mijin saboda rashin kaurin ruwan maniyyi da yake fama da shi.
Matar auren mai suna Salamat Suleiman da suka yi aure watanni biyu da suka gabata ta damu mijinta ya saketa sakamakon rashin lafiyarsa.
Ta sanarwa da wata kotu dake a garin Ilorin cewa ta fuskanci mijinta bashida lafiyayyan maniyyi, hakan yasa ta nemi kotu da ta raba aurensu domin ta gaji da zama dashi.
Koda Kotun ta tuntubi wanda ake kara ya bayyana cewa yana da matsala takes lafiya, amma yace ita ma matarsa tana da matsalar lafiya.
Ya kara da cewa duk dama haka yana son matarsa, ya nemi kotu da Kada ta raba auren ta barsu su je su daidaita a tsakanin su.
Hakan yasa alkali Abdulkadir Umar yaiwa matar bayani cewa ta yi hakuri su je su nemi taimakon samun lafiyarsu wajen Likita.
Ya nemi matar da ta kara baiwa mijin dama ta karshe domin ci gaba da zaman auresnu domin kowane aure yana da nasa matsalar.
Kotun ta dage karar har zuwa 28 ga Watan Augusta domin jin yadda zamansu ya kasance don sanin matakin da Kotun ta ta dauka.