Maganin Karin Ruwan Maniyyi Sosai Don Ma'aurata - Android Pols
'Yan uwa ina yiwa kowa fatan Alkhairi, a yau insha Allah zan baku wani babban sirrin ga masu fama da matsalar karancin ruwan maniyyi. 


Ko wanda maniyyin nasa matattun sunfi masu rai yawa, ko wadanda maniyyin nasu baya fita yadda ya kamata to ga wannan fa'ida ayi kokari a jarraba ta insha Allah za a dace.


Wannan hadin yana kara:


Motility

morphology 

Da kuma sperm count

Abinda Za'a Nema sune kamar haka:


Za'a samu 'ya'yan kabewa, amma kabewar wacce ta nuna sosai sai a gyara su a shanya su bushe a inuwa bayan nan za a dake su sosai su zama gari.


Za'a rika diban karamin chokali (teaspoon)ana zubawa a madara da ruwa peak milk rabin gwangwani a sha safe da yamma.


Idan peak tana bata maka ciki sai ka samu nono mai kyau mara tsami ka hada dashi kana sha, sannan za'a sha wannan tsawon sati 3 zuwa wata guda.


Amma idan mutum Allah bai bashi haihuwa ba sandiyyar karanci ko tsinkewar maniyyi, sai ya rika hakurin rage Jima'i, ya rika yi kamar sau 2 ko 1 a sati, domin wannan shine zai bawa maniyyi damar zama cikakke wanda zai iya samar da 'da.


Allah yasa mu dace. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post