Illolin Gishiri: Yadda Jikin Dan Adam Ke Sauyawa Sakamakon Cin Gishiri Da yawa




A cewar Wikipedia, Gishiri yana a matsayin ma'adinai wanda ya ƙunshi sodium da chloride, wani sinadari na babban nau'in gishiri. 


Ana amfani da gishiri a matsayin ɗanɗano. Ana kuma amfani da shi wajen samar da wasu abubuwa kamar rini, tukwane, sabulu, da chlorine. An fi yin amfani da gishiri a masana'antu a matsayin sinadarai. 


Baya ga haka kuma Jiki yana buƙatar gishiri don samun daidaiton ruwa da aikin jijiya, amma gishiri da yawa na iya zama haɗari ga jikin dan adam. 


Gishiri ya ƙunshi 40% sodium da 60% chlorine. Yawan sodium na iya haifar da hawan jini, duwatsu a cikin koda, da cututtukan zuciya. Ƙananan sodium na iya haifar da yawan jiri da Karancin gudanar jini ga jiki. 


A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, yawan gishirin da kuke ci a kullum bai kamata ya wuce 1.5g ba, ko fiye da rabin teaspoon(cokali). 


Lokacin da kuka yi amfani da fiye da adadin da aka ba da shawarar ku yi, zai iya zama haɗari ga lafiyar ku. Ga wasu alamomi guda biyar da za ku gane kuna cin gishiri da yawa a jikin ku:


1) Yawan Jin ƙishirwa Koda Yaushe 

Nazarin ya nuna cewa abinci mai yawan sodium na iya shafar ma'aunin ruwan jiki. Lokacin da kuka ci gishiri da yawa, za ku iya jin ƙishirwa a mafi yawan lokaci. Shan isasshen ruwa shine hanya mafi kyau don samun daidaito. Jikin ku zai ci gaba da nuna cewa yana buƙatar ƙarin ruwa don dawo da ma'aunin gishiri. Ana kuma ba da shawarar ku guji sarrafa abinci da gishiri mai yawa maimakon haka ku yawaita cin kayan lambu da 'ya'yan itatuwa. 


2) Hawan jini 

Yawan shan gishiri na iya tayar da hawan jini. Hawan jini yana faruwa ne sakamakon karuwar adadin jinin da ke tura bangon magudanar jini. Sodium galibi ana samunsa ne a cikin jinin mutum, inda yake jan ruwa. A sakamakon haka, idan kuna cin sodium da yawa, jinin ku zai bukaci ruwa mai yawa. 


3) kumburin ciki

 Yin amfani da gishiri da yawa zai iya sa ku ji kumburin ciki saboda gishiri yana jawo ruwa. Idan kuna cin gishiri da yawa, mai yuwa za ku fuskanci riƙewar gabobi da kumburi a wasu wurare na jikin ku, misali, yatsu ku na kafa da na hannu. 


4) Ciwon kai 

 Idan kuna cin gishiri da yawa, za ku iya fuskantar ciwon kai akai-akai. Cin abinci mai gishiri na iya haifar da ciwon kai kuma yana haifar da yaduwar jini a cikin kwakwalwa, wanda zai iya haifar da yawan ciwon kai akai-akai. 


5) Yawan fitsari 

Daya daga cikin alamun da ke nuna yawan shan gishiri shine yawan yin fitsari. Wani lokaci, shan gishiri da yawa ba zai zama sanadin yawan fitsarin ku akai-akai ba. Cin gishiri da yawa kuma yana iya zama sanadin hakan. Don dakatar da hakan, yana da kyau ku rage yawan cin gishirin da kuke ci sannan kuma ku dinga shan ruwa mai yawa don kawar da gishirin da ya wuce kima a jikin ku. 


Da fatan kun ilimantu daga wannan takaitaccen fadakarwa akan yawan cin gishiri. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post