Innalillahi Wa'inna Ilaihin Rajiun! Dukkan mai rai mamaci ne, dubban jama'a na cigaba da nuna alhinin su kan rasuwar hazikin matashi dan gwagwarmaya a Kafar soshiyal midiya Auwal G Danbarno.
Ya rasu ne a ranar Lahadi sakamakon hatsarin mota. Kafin rasuwarsa sai da yai rubutu a shafinsa na Facebook inda yake yin addu'a kan Allah ya jikan wadanda suka mutu a sakamako fadowar gini a filin idi na Kano.
Ga rubutun da ya wallafa.
Tun bayan sanar da mutuwarsa mutane da yawa na ta bayyana alhinin su. Da fatan Allah yasa jikinsa yai masa rahama amin.