Amfanin Da Shan Ruwa Akai-akai Ke Yi Ga lafiyar jikin Dan Adam - Android Pols
Ana bukatar mutum ya dinga shan ruwa akai akai, domin masana kiwon lafiya sun bayyana cewa shan ruwa akai-akai na yaki da cututtuka da dama.


Musamman shan ruwa da safe kafin aci komai na da fa'ida kamar haka:


1- Shan ruwa da sassafe na samarwa da jikin dan Adam karin ruwa, duba da irin sa’o’in da aka dauka ana bacci.


2-  Shan ruwa kafin a ci abinci da safe na kara karsashi da karfin jiki. 


3- Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tada kwakwalwa.


4- Shan ruwa da sassafe kafin a ci komai na tsaftace jiki daga cutuka.


5- Shan ruwa da sassafe kafin a ci abinci na yakar cutuka tare da kara garkuwa ga jikin dan Adam.


6- Shan ruwa da sassafe yana sa narkewar abinci kamar yadda ya dace. 


7-  Hakazalika, yana sa a rage kiba, ga masu muguwar kiba. 


8- Yana gyara launin fata tare da sanya walwalin fata da walkiya. 


9- Yana kariya daga ciwon koda tare da tsaftace mafitsara daga kwayoyin cuta. 


10- Shan ruwa da safe kafin cin abinci na taimakawa tsawon gashin kai tare da walkiyarshi. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post